Nasarar da jigon APC Bola Tinubu ya samu a zaɓen fidda-gwanin takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC, ta yi daidai da karin maganar da Hausawa ke cewa, ‘alheri danƙo ne, ba ya faɗuwa ƙasa banza.
Tinubu ya samu gagarimar nasara kan sauran ‘yan takarar da su ka ƙi janye masa, bayan APC ta amince a miƙa takara Kudu, a kudun ma aka tsamo mutum biyar aka ce a cikin su za a fidda gwani.
Tinubu ya samu ƙuri’u 1271.
Ko shakka babu Tinubu ya samu gagarimin goyon bayan gwamnonin Arewa, waɗanda su ka amince a miƙa mulki kudu, sai kuma ɗimbin magoya baya daga yankin Kudu maso Yamma, yankin da Tinubu ya fito, kuma inda ya fi dasa yaran sa, har su ka yi yaɗo da yabanya sosai.
Magoya bayan sa sun saka masa daga sama zuwa ƙasa kan wakilan zaɓe, inda su ka fassara duk wani Bayarabe da ya fito takara tamkar maci amanar Tinubu.
Sun nuna wa Matakimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo haka a fili, cewa maci amana ne, ganin yadda ya fito takarar shi da ubangidan sa, Tinubu.
Bola Tinubu ya kusa kifar da garin sa a cikin rairayi sakamakon gorin kasa cin zaɓe da ya yi wa Shugaba Buhari.
Duk da cewa ya samu gagarimin rinjaye, an yi zaton Tinubu ba zai kai labari ba, ganin yadda tun farkon fitowar sa takara aka riƙa yi masa yarfen cewa ya tsufa, karkarwa ya ke yi, ba shi da lafiya, sannan kuma an riƙa tuna irin yadda ya cika motoci da kuɗi a ranar jajibirin zaɓen 2019.
2023: Gurugubji Faɗan Dattawa:
A yanzu dai zaɓen 2023 ya nuna cewa akwai aiki a gaban Tinubu, domin zai yi kokawa ce da Atiku Abubakar na PDP da kuma Rabi’u Kwankwaso na NNPP.
Idan ‘yan Arewa su ka ƙi zaɓen APC saboda haushin an bai wa Kudu maso Yamma takara, to Atiku zai iya kayar da Tinubu warwas.
Haka nan idan Kwankwaso ya mara wa Atiku baya, to nan ma Tinubu sai dai ya yi haƙuri.
Ko ma ya zaɓen 2023 zai kaya, akwai sauran jan aiki a gaban Tinubu, wanda ko a zaɓen wanda zai zame masa mataimaki ma akwai wata sabuwar rigimar a kwance?
Shin Musulmi Tinubu zai ɗauka mataimaki kamar yadda ya ke Musulmi? Ko kuwa Kiristan Arewa Tinubu zai ɗauka.
Duk wanda Tinubu ya ɗauka a cikin waɗannan mutum biyu, to ya buɗe ƙofar wani sabon ce-ce-ku-ce kenan.