Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa akwai buƙatar a shata tsari a cikin gaggawa domin gyara da kula da yawan jama’a a Najeriya, ta yadda yawan zai zama alheri ba alaƙaƙai ba.
Osinbajo ya ce maganar gaskiya yawan jama’a a Najeriya ka iya zama tamkar wani bam da aka turbuɗe a cikin ƙasa, wanda lokaci kawai ya ke jiran ya cika, ya fashe daram!
Da ya ke magana a wurin wani muhimmin taron Makomar Inganta Sabon Tsarin Yawan Jama’a, Osinbajo wanda Mai Baiwa Shugaban Ƙasa Shawara a Fannin Inganta Rayuwar Jama’a, Maryam Uwais ta wakilta, ya ce “idan aka kula da yawan jama’a ta yadda za a ci moriyar jihar, to alheri ne. Amma fa idan aka bar tsarin yawan jama’a sakaka babu saiti, yawan zai zama taron yuyuyu, kuma zai kasance wani bam ne da ke turbuɗe cikin ƙasa, wanda lokaci kaɗai ya ke jira ya cika ya fashe daram!”
Daga nan sai ya ce akwai buƙatar a zuba jari sosai a cikin jama’a domin a ci moriyar yawan, don kada yawan ya zama haihuwar yuyuyu.
“Masana sun sha nuna cewa yawan jama’a ba matsala ba ce, matsalar ita ce rashin tsarin da zai sa a ci moriya da alfanun yawan a wajen inganta rayuwar jama’a da kuma bunƙasa ƙasa.”
Osinbajo wanda Farfesa ne a fannin shari’a, ya lissafa muhimmancin yawan al’umma a cikin ƙasa, inda ya ce akwai samun kuɗaɗen haraji mai yawa, samar da kayan amfani da sarrafa abubuwa da yawa, samar da ma’aikata masu yawan gaske da sauran su.
“Sai dai kuma idan ba a yi tsarin da za a bi a ci moriyar yawan jama’a ɗin ba, to kuwa tabbas yawan zai zame mana alaƙaƙai ya haddasa yawan masu aikata laifuka, yawan marasa aikin yi da cima-zaune, gurɓacewar muhalli, ƙarancin abinci, takura wa albarkatun ƙasa, ƙarancin muhalli, cinkoson motoci da cinkoson birane, matsalar tsaro, ƙarancin wadatar jari da rashin kwanciyar hankali.” Cewar Osinbajo.
Discussion about this post