Rundunar ‘yan sandan jihar Abia ta bayyana cewa ‘yan bindiga sun sako babban limamin cocin Methodist Samuel Kanu-Uche tare da wasu limamai biyu da suka yi garkuwa da su a jihar.
Bishop din dayoyis din Owerri Dennis Mark da mataimakinsa Kanu, Shitti na cikin fastocin da ‘yan bindigan suka sace tare da babban limamin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Geoffrey Ogbonna ya sanar da haka a garin Umuahia ranar Litini.
Ogbonna ya ce bashi da masaniya ko an biya kudin fansa kafin aka sako limaman.
Idan ba a manta ba PREMIUMTIMES ta buga labarin cewa ‘yan sun yi garkuwa da babban limamin cocin Methodist Samuel Kanu tare da wasu Limamai biyu a hanyar Enugu zuwa Fatakwal dake karamar hukumar Umunneochi a jihar Abia.
Maharan sun yi awon gaba da Bishop din Owerri na cocin Methodist Dennis Mark sannan da Wani limamin Kuma mataimakin Kanu a ranar Lahadi da rana.
Majiya da dama sun bayyana cewa an yi garkuwa da limaman yayin da suka hanyar zuwa wani taro a jihar Abia.
Kafin a sako su maharan sun bukaci a biya su Naira miliyan 100.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Geoffrey Ogbonna Shima ya tabbatar da haka sannan ya ce rundunar ta fara farautan ‘yan bindiga domin ceto limaman