Fitaccen malamin addinin Muslunci, Sheikh Ahmed Gumi ya tattauna da ƴan bindigan da suka sace matafiya a jirgin kasan Kaduna-Abuja inda suka saki mutum 11 cikin su.
Idan ba a manta a cikin watan Maris ƴan bindiga sun tada da nakiya a layin jirgin kasa inda suka kashe matafiya 9 suka sace mutane sama da 60.
Tun bayan wancan lokaci, maharan ke tattaunawa da gwamnati amma abin bai yiwu ba.
A ranar Asabar sun saki mutum 11 cikin waɗanda ke tsare a hannun su.
Kakakin Gumi, Tukur Mamu ya shaida cewa ƴan bindigan sun ce Gumi ne kawai zai faɗi musu inda za su ajiye mutanen, inda shi kuma ya amince a ajiye su a dajin Kudenda.
Mamu ya ce shehin malamin na cigaba da tattaunawa da ƴan bindigan domin ganin an sako sauran fasinjojin dake tsare a hannun su.
Akwai mutum sama da 50 da ke tsare har yanzu a hannun ƴan bindigan da ba a sako su ba.
Sunayen fasinjojin da aka saki
Jessy John, Amina Mohammed (Gamba), Rashida Busari, Hannah Ajewole, Amina Jibr, Najib Daiharu, Gaius Gambo, Hassan Aliyu, Peace Boy da Danjuma Sa’idu.