Ƴan bindiga sun kashe mutum biyu, sun yi garkuwa da wasu mutum 22 ciki da ƴanngida ɗaya su 13 a babban birnin tarayya Abuja.
Maharan sun afka kauyen Rafin Daji dake gundumar Abaji inda suka yi awon gaba da maza, mata da yara kananan dake aiki a gonakinsu da rana tsaka.
‘Yan bindigan sun kai wa kauyen hari ranar Larabar da ta gabata amma ba sanar ba sai da rundunar ‘yan sandan Abuja ta sanar ranar Juma’a.
Rafin Daji kauye ne dake da iyakan ƙasa da karamar hukumar Lapai dake jihar Neja.
Maharan sun kona taraktoci biyu na wani babban manomi a kauyen sannan daga cikin mutum 22 din da suka yi garkuwa da su mutum 13 ‘yan gida daya ne.
Wani Ibrahim Barde dan uwan daya daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su ya tabbatar cewa Fulani ne suka yi garkuwa da mutane.
Barde ya kuma ce ƴan bindigan sun bukaci a biya su naira miliyan 12 kafin su sako mutane 22 da suka yi garkuwa da su.
Kakakin rundunar ƴan sandan Abuja Oduniyi Omotayo ya tabbatar da aukuwar lamarin da ya ke amsa tambayar da PREMIUM TIMES ta yi masa game da abinda da ya faru ranar Asabar.
Ya ce zuwa yanzu babu wanda aka ceto daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su.
Omotayo ya ce rundunar ta hada hannu da mafarauta domin kamo maharan da ceto mutanen da suka yi garkuwa da su.
Kauyukan dake gundumar Abaji sun yi fama da garkuwa da mutane a cikin kwanakin da suka gabata.
Discussion about this post