Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta bayyana cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da dagacen kauyen Zira Yahaya Abubakar da dansa Habibu Sale a karamar hukumar Toro.
Kakakin rundunar Ahmed Wakili ya sanar da haka wata sanarwa ranar Litinin.
A kauyen Zira a kwai ofishin ‘yan sanda dake Rishi sannan kauyen na da iyakan ƙasa da jihar Filato.
Maharan sun afka kauyen da misalin karfe 2 na daren Asabar.
Wakili ya ce tuni rundunar ta fara farautar maharan domin kamo su da ceto mutanen da suka yi garkuwa da su.
Ya yi kira ga mutane da su taimaka wa jami’an tsaro da duk bayanan da zai taimaka wajen kamo maharan.
“Muna kira ga mutane da su kwantar da hankulansu cewa nan ba da dadewa ba za a ceto dagacen da dansa daga hannun ‘yan bindiga.
Idan ba a manta ba an ruwaito yadda ƴan bindiga suka yi awon gaba da dagacen kauyen Panyam dake karamar hukumar Mangu a jihar Filato
Mazauna kauyen Panyam sun ce maharan sun waske da Adamu Derwan a safiyan Litini.
Kakakin ‘yan sandan jihar Alfred Alago shi ma ya tabbatar da haka ranar Litini da yamma.
Ya ce tuni kwamishinan ‘yan sandan jihar ya aika da ma’aikata domin a kamo maharan da kuma a ceto wanda aka yi garkuwa da su.
Alago ya yi kira ga mutane da su taimaka wa jami’an tsaro wajen basu bayanan sirri domin a dakile hare-haren ƴan bindiga.
Discussion about this post