Wasu ƴan ɗaurin aure sun faɗa hannun ƴan bindiga a hanyar dawowa daga Sokoto wajen ɗaurin auren abokin su.
Kakakin Kungiyar matafiyar waɗanda masu sana’ar saida waya ne Ashiru Zurmi ya ce mutum 20 sun arce a daga hannun ƴan bindigan a lokacin da suke nausawa da su cikin daji.
“Mota ce ta lalace a a Tureta. Makanike ya zo ya gyara ta, duka-duka ba a wuce mintuna 40 ba a ka ci gaba da tafiya. A daidai kusa da Bakura daga Tureta sai ƴan bindigan suka dira wa motar.
” Abinda muke zato shine akwai waɗanda suka sanar wa ƴan bindigan labarin waɗannan matafiya. Lallai akwai domin ga dukkan alamu hakan ne ya faru.
” Mutum 20 cikin 50 din da su arce da su sun gudu. Duk kuma sun iso gida wasunsu da rauni a jika.
Zurmi ya kara da cewa ƴan bindigan sun kira waya amma basu faɗi nawa za abiya su kuɗin fansa ba.
Discussion about this post