A ranar Alhamis da rana ce ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya gabatar da Gwamnan Delta Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakin takarar shugaban ƙasa ɗin sa a zaɓen 2023 mai zuwa.
Ɗaukar Ifeanyi Okowa matsayin mataimakin takarar shugaban ƙasa na PDP zai haifar da abubuwa da dama, waɗanda ko dai su kai Atiku ga nasara, ko kuma ya ƙara shan kaye, kamar yadda ya sha a baya har sau uku a zaɓen shugaban ƙasa.
Ko ma dai me kenan, lamarin zai yi tasiri ne ko rashin yin tasiri, bisa la’akari da irin yadda yi amfani da abubuwan.
Da farko dai masu ruwa da tsaki na yi wa Okowa kallon cewa natsatstsen mutum ne kuma kamili, ba kamar Gwamna Nyesom Wike da ake wa kallon ɗan gidoga ko ɗan hauragiya da harigido ba.
Can a jihar Delta dai lamarin siyasar za ta iya canjawa idan PDP ta samu nasarar kama mulki. Domin tun daga 1999 har yau tsohon Gwamna James Ibori ne ke yin uwa-makarɓiya wajen naɗa wanda zai yi gwamna a jihar.
Shi kan sa Okowa yaron gidan siyasar James Ibori ne, saboda a 1999 zuwa 2007 ya yi kwamishina ƙarƙashin gwamnatin James Ibori. Kuma ya yi Sakataren Gwamnatin Jihar Delta a zamanin gwamnatin Emmanual Uduiaghan.
Cikin 2011 Okowa ya ci zaɓen Sanata na Delta ta Arewa.
Sai dai kuma an samu saɓani a wannan zaɓen fidda-gwani na wanda zai gaji Okowa a gwamnan Delta ƙarƙashin PDP. Wanda Ibori ke so daban, shi ma Gwamna Okowa wanda ya ke so daban. Dukkan su kuma ƙabilar Urhobo ne, tushen James Ibori.
A ƙarshe dai ɗan takarar da Okowa ke so ya kayar da ɗan takarar da Ibori ke su. An ce Ibori ya fusata, har ya yi alƙawarin idan zaɓe ya zo sai ya shuka wa PDP ko kuma ɗan takarar tana jihar tsiya.
To yanzu dai tunda an zaɓi Okowa ɗan takarar mataimaki, jam’iyyar PDP ta koma a hannun sa kenan a jihar Delta, maimakon ubangidan sa James Ibori.
Abu na biyu shi ne ana ganin matsayin Okowa ɗan asalin ƙabilar Igbo, hakan zai iya yayyafa wa yankin Kudu maso Gabas ruwan sanyi, su haƙura su goyi bayan PDP, tunda dai ba su samu damar tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa ba a manyan jam’iyyu biyu, APC da PDP.
Amma shi kuwa Wike, ba sau ɗaya ko sau biyu ba ya sha nesanta kan sa ko asalin sa daga kabilar Igbo.
Sannan an ce Wike ne ya riƙa sukar Peter Obi har ya harzuƙa shi, ya fice daga PDP, ya koma LP ya fito takarar shugaban ƙasa.
Okowa bai cika surutai ko bobbotai irin na Wike ba. Ana ganin Wike ya yi katoɓara a shekarun baya da ya ce “Jihar Ribas ta Kiristoci ce zalla.”
Shi kuwa Gwamna Okowa babu ruwan sa da shiga-sharo-ba-shanu, ko yin uwa-makarɓiyar rigingimun siyasa, kamar yadda Gwamna Wike ke yi, har abin ya zame masa jiki.
Babban aikin da ke gaban Okowa shi ne yadda zai samar wa PDP ƙuri’u a Kudu maso Gabas, Kudu maso Yamma da Kudu maso Kudu. Zai iya yin bakin ƙoƙarin sa, musamman tunda bai taɓa shiga hancin manya da ƙudundune ba.
An haifi Okowa a cikin 1959 a garin Owa-Alero, cikin Ƙaramar Hukumar Ika ta Arewa maso Gabas.
Sai dai kuma masu nazarin siyasa da dama na ganin a yanzu PDP za ta iya rasa ɗimbin ƙuri’un magoya bayan Gwamna Wike, ganin yadda ya samu ƙuri’u da dama a zaɓen fidda gwani.
Su na ganin da shi aka ɗauka, zai fi karɓuwa har a Arewa sosai. Domin a cewar da dama, ba a san Ifeanyi Okowa a Arewa ba.
Ya yi kwamishina zamanin mulkin James Ibori, ya yi Sakataren Gwamnatin Jiha zamanin mulkin Emmanual Uduiaghan, kuma ya yi sanata kafin ya zama gwamna.