Bashir Maru, tsohon mataimakin shugaban ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar Zamfara, ya zargi Gwamna Matawalle da yi wa abokan sa da dangin sa watandar motocin da aka sayo domin bayarwa ga jami’an tsaro.
Cikin wata sanarwa da Kari ya fitar, ya zargi Bello Matawalle da shirya wata maƙarƙashiyar yunƙurin kama shi.
Ya ƙara da cewa ya na da hujjojin da ke nuna dukkan waɗanda aka yi wa watandar motocin ƙirar Hilux.
Maru dai kwanan nan ne ya sauka daga muƙamin sa na Babban Sakataren Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Zamfara, domin ya shiga takarar Mamba na Majalisar Tarayya da nufin wakiltar Maru da Bunguɗu, a ƙarƙashin APC.
Sai dai kuma kunnuwan gari sun ce Gwamna Matawalle ya ce a bayar da takarar ga wai yaron tsohon Gwamnan Zamfara Abdul’aziz Yari, a matsayin hanyar sasantawa tsakanin Yari da Matawalle.
Amma kuma Maru ta je ya shiga takara, duk da roƙon da Gwamnan da sauran jiga-jigan jam’iyya su ka yi masa cewa za a bayar da takarar ga wanda su ka cimma yarjejeniyar za a damƙa wa.
Maru an ce ya faɗi zaɓe, Abdumalik Zanna ya yi nasara.
To dama kafin zaɓen fidda gwani, Maru ya zargi wasu na ƙoƙarin sace shi saboda jajircewar da ya yi cewa sai ya shiga takara. Hakan ne ya sa ya ɓoye aka rasa jin inda ya ke, don gudun aka a yi masa lahani.
Batun Watandar Motocin Tsaro:
A rubutun da ya yi a shafin sa na Facebook, Maru ya ce Matawalle ya yi watandar motoci ga abokan sa da dangin sa, kuma motocin an sayo su ne don inganta tsaro da nufin rabawa ga jami’an tsaro.
A ce an sayo motocin ne daga kuɗaɗen karo-karo na Asusun Haɗaka na Jiha da Ƙananan Hukumomi.
Ya ce an sayo motoci 200, an raba 120 ga ‘yan sanda, Sojojin Sama da na Ƙasa da sauran ɓangarorin jami’an tsaro masu sa khaki.
“Amma abin takaici, kashi 35 zuwa kashi 40 cikin 100 na yawan motocin duk Matawalle ya yi watandar su ga abokan sa, makusanta da kuma dangin sa a Kano, Kogi, Osun Nasarawa, Abuja, Barno, Adamawa, Zamfara da sauran wurare daban-daban.
“Nan ba da daɗewa ba zai fito da dalla-dallar waɗanda aka yi wa watandar, domin jama’a su gani kuma su san abin da ke faruwa a bayan idon su.”
Ya ce abin takaici kuma waɗanda aka yi wa watandar motocin duk sun sayar da su arha takyaf sun kaɗas da kuɗaɗen.
Daga nan ya ƙalubalanci gwamnan ya fito da ko da kashi 15 bisa 100 ne na motocin da aka sayo a Zamfara, daga ranar 29 Ga Mayu, 2019.