Tseren zama shugaban ƙasa a zaɓen 2023 ya shiga sabon zango ga ‘yan takarar ta zaɓen da za a gudanar a ranar 25 Ga Fabrairu, 2023.
Yayin da PDP ta fara fitar da na ta ɗan takarar, wato Atiku Abubakar, ita kuwa APC ta tsayar da Bola Tinubu.
Waɗannan ‘yan takara biyu, su ne a sahun gaba, amma kuma Rabi’u Kwankwaso na NNPP da Peter Obi na LP za su iya hana masu ruwa gudu, kuma su zame masu ƙarfen ƙafa.
Har yanzu dai ana kan ƙoƙarin fitar da waɗanda za a tsayar a mataimakin shugaban ƙasa a cikin jam’iyyun.
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) dai ta ce duk jam’iyyar da ba ta miƙa sunan mataimakin takara ba, to za a hana ta shiga zaɓen shugaban ƙasa.
Kuma an yarda daga nan har zuwa 15 Ga Yuli za a iya sauya sunan ɗan takara, a maye gurbin sa da wani, bisa wasu dalilai da INEC ta amince da su.
‘Yan Takarar Shugaban Ƙasa:
Baya ga Atiku, Kwankwaso, Tinubu da Obi, wasu jam’iyyu 10 sun shiga takarar, kamar Malik Ado-Ibrahim na YPP, Omoyele Sowore na AAC, Adewale Adebayo na SDP, Kola Abiola na PRP, da Hamza Al-Mustapha na AA.
Akwai kuma wasu mutum biyar daga jam’iyya daban daban masu neman kujerar shugabancin Najeriya.
Atiku Da Tinubu Na Cikin Tsaka-mai-wuyar Neman Ɗan Takarar Mataimaki:
Yayin da Atiku ya cika ruwan ido kan wanda zai ɗauka, ya na shan matsin lamba cewa ya ɗauki wanda ya zo na biyu, wato Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas.
Yayin da wasu kuma ke ba shi shawara cewa ya ɗauki Gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta.
Wasu kuma na ganin har gara ya ɗauki Gwamna Udom Emmanuel na Akwa Ibom. Wasu kuwa cewa su ke yi ya ɗauki tsohon Gwamnan Imo, Emeka Ihedioha ko tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Pius Anyim, ko Peter Obi shi kan sa.
Da alama dai Atiku daga cikin Shiyyar Kudu maso Gabas zai ɗauki ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa kenan, kasancewar sa daga Arewa kuma Bafulatani.
Peter Obi wanda ya yi wa Atiku Abubakar takarar mataimakin shugaban ƙasa a 2015, ya fice daga PDP kwanaki kaɗan kafin ranar zaɓen fidda-gwani na ‘yan takara, ya koma LP, inda aka ba shi takarar shugabancin ƙasa.
Ana ganin idan ‘yan ƙabilar Igbo su ka juya wa PDP baya, su ka zaɓi LP ta Obi, to tabbas PDP za ta fuskanci zaizayewar ƙuri’u.
Tinubu Ya Tuma Tsalle Cikin Tafkin Ƙaƙa-ni-ka-yi:
Manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa sun tambayi Tinubu sunan ɗan takarar sa na mataimakin shugaban ƙasa, a lokacin da ya kai wa Shugaba Muhammadu Buhari ziyara. Sai cewa ya yi: “Ba zan faɗa maku sunan sa ba. Amma dai yanzu haka sunan na sa na cikin aljihu na.
Kafin sannan, Kakakin Kamfen ɗin sa, Bayo Onanuga, ya sanar cewa daga cikin gwamnonin Arewa Tinubu zai fitar da mataimakin takarar sa.
Tabbas fitar da mataimakin takara zai fi yi wa Tinubu wahala fiye da Atiku. Tinubu dai Musulmi ne daga Kudu maso Yamma. Shin zai zaɓi musulmi daga Arewa ya yi masa mataimaki ne? Ko kuwa Kiristan Arewa zai ɗauka, wanda hakan ana ganin idan ya yi ɗin zai haifar masa da matsala daga Arewa?
Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN dai a ranar Juma’a ta fitar da sanarwa ta hannun Sakataren CAN na Ƙasa, Joseph Daramola, inda ta nemi Tinubu ya yi adalci ya zaɓi Kirista, don a yi raba-daidai.
Haka nan su ka yi kira ga Atiku shi ma ya ɗauki Kirista a matsayin mataimakin shugaban ƙasa, shi kuma Peter Obi ya ɗauki Musulmi daga Arewa.
Idan Tinubu ya ƙi ɗaukar mataimaki daga Arewa maso Yamma, to zai fuskanci matsala, domin ‘yan yankin za su ga cewa Kwankwaso kaɗai ne ɗan takara daga cikin su, don haka za su goyi bayan sa.
Kuma dama daga Arewa maso Yamma ne aka fi samun ruwan ƙuri’u, musamman a Kano, jihar da Kwankwaso ya fito.