A ranar Lahadi ne rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta tsinci gawar wani mutum da ya rataye kansa a jikin itace saboda buduewar sa da yake tsananin so ta auri wani.
‘Yan sanda sun tsinci gawar wannan mutum ne a kauyen Kanti dake karamar hukumar Kazaure.
Mazauna kauyen sun ba su gane ko wanene shi ba amma dai an tsinci wani katin aure a cikin aljihunsa.
Kakakin rundunar Lawan Adam ya bayyan cewa sakamakon binciken da rundunar ta gudanar ya nuna cewa sunan mutum Ibrahim Adamu Mohammed mai shekaru 42.
Adamu ya ce Mohammed mazaunin garin Kano ne.
‘Yan uwan mutumin daga Kano sun bayyana cewa mamacin ya kashe kansa bayan ya samu katin gayyatar auren budurwarsa dake jihar Jigawa.
“Bayan ya gano gaskiyar lamarin sai ya kashe kansa ta rataya a jihar.
Zuwa yanzu gawar mutumin na ajiye a dakin ajiyan gawa dake asibitin Kazaure.
Discussion about this post