A nan Najeriya wani basaraken ƙauye ya ƙirƙiri ‘kuɗaɗen’ da ake mu’amalar kasuwanci da cinikayya da su a yankin kasuwar masarautar sa, domin bunƙasa tattalin arzikin yankin masarautar.
Wakilin mu ya fara cin karo da wata mata mai suna Silifatu Adefila a cikin watan Fabrairu, lokacin da ta ke gaggawar tafiya zuwa kasuwar Oja Oba, sabuwar kasuwar da basaraken ƙauyen, wato Olusin na Ijara -Isin.
Wannan ƙauye dai ya na cikin Jihar Kwana ne.
Saurin da Silifatu ke yi a ranar da wakilin mu ya ci karo da ita, shi ne ta na so ne ta isa kasuwar da wuri, domin ta karɓi ‘kuɗin’ da basaraken ƙauyen ke rabawa a kowace ranar Asabar.
Idan ta samu karɓar kuɗin a hannun Kabiyesi, sun ishe ta sayen cefanen gidan ta na sati ɗaya.
“Wasu kuɗaɗe ne ya ke rabawa, waɗanda ba za ka iya kashe su ba, sai a cikin kasuwar Ojo-Oba kaɗai. Amma yawancin kantinan cikin ƙauyen na karɓar kuɗaɗen.” Inji ta.
Ademola Ajibola shi ne Basaraken ƙauyen, ya shigo da wannan tsari cikin Agusta, 2021, a matsayin hanyar musayar kuɗaɗe cikin Ijara -Isin.
Yayin da wasu masana tallalin arziki ke jinjina masa, ganin yadda ya samar da hanyar rage wa al’ummar su cunƙin raguwa, wasu kuma na ganin kishiyar hakan, wato su na sukar sa.
Hukumar Ƙididdigar Alƙaluma ta Kasa (NBS) ta bayyana cewa aƙalla mutum miliyan 91 na fama da ƙuncin rayuwa a Najeriya.
Wannan adadi kuwa ya ƙaru ne sanadiyyar ƙarin farashin kayan abinci da kashi 20 bisa 100.
Sabon Sarkin Ƙauyen Da Ke Kishin Inganta Rayuwar Jama’ar Yankin Sa:
Ƙaramar Hukumar Isin na cikin Jihar Kwara ne, inda ma’aikatan gwamnati da jami’an kula da lafiya da manoma ne ke da ƙarfin iya yin hada-hadar kuɗaɗe.
An fi noma kashu a garin, inda bokitin kashu kan kai Naira 4,000 ko 3500.
Raja’a da noman kashu ne ya sa farashin kayan abinci ya tashi a yankin.
A ƙauyen ana yin sana’ar POS, inda ake cire ladar naira 30 a cikin kowace Naira 1,000 da aka cira.
Amma an fi amfani da POS wajen cirar kuɗi, ajiya da aika wa wani.
Idan za a yi hada-hadar banki tilas sai mutanen garin sun je Omu-Aran, tsohuwar hedikwatar su, ko kuma su zarce Ilorin kai-tsaye. Saboda a shekarun baya sun sha fama da ‘yan fashi, har aka rufe bankuna a Oro, Omu-Aran, Offa da sauran garuruwan da ke kan titin zuwa Kabba.
Rayuwar Al’ummar Masarautar:
Mazauna yankin na fama da matsanancin hali, amma bayyanar basaraken ta na taimakawa sosai a Ijara.
Saboda ya na taimaka wa tattalin arzikin yankin, gyaran makarantu, titina da hanyoyi, da kuma kammala gidaje masu sauƙin kuɗi wadanda gwamnatin tarayya ta fara ginawa tun lokacin mulkin Shehu Shagari, amma ba ta kammala ba.