Daga ina zan dauki mataimakina? Wannan ita ce damuwar Bola Ahmed Tinubu, dantakarar shugaban kasa a APC, a yanzu.
Ba kamar Atiku na PDP ba, wanda kai tsaye ya san daga kudancin Nijeriya zai dauko nasa, kuma Kirista, walau daga cikin Inyamurai ko daga y’an Neja Delta.
Shi Tinubu yana tsaka mai wuya. A Arewa wa zai dauka? Musulmi ko kirista?
Mutanensa Kirista irin su Babachir Lawal sun ce in ya dauki Musulmi tabbas ba zai ci zabe ba, saboda Kiristoci za su gwammace zabar Atiku wanda yake da Kirista mataimaki. Suna ganin lokaci ya canza ba kamar zamanin Abiola da Kigibe ba.
A daya bangaren kuwa, idan Tinubu ya dauki Kirista, to Musulmi yan’arewa wadanda su ne wadanda suka fi yawa a Arewa za su ga cewa an mai da su tsiraru, yankallo, abunda ba a taba yi ba a mulkin Nijeriya. Haka zai sa su runtuma wajen Atiku.
Da na sa wannan rubutu a Facebook, wani maibibiya ta ya ce dole Tinubu ya zabi dayan biyu: Idan adalci yake so, ya dauki Kirista; idan kuwa cin zabe yake so, to, ya dauki Musulmi. A yanzu wanne ne TInubu ke bukata: adalci ko cin zabe? Kar kuma ya yi kamun gafiyar ‘Baidu.
Da alama dai duk inda Tinubu ya yi, Atiku zai ce gaba ta kai shi. Ga shi magudi yana kara wuya. Ga shi ba zaben fid da gwani ba ne na mutane kalilan balle a ce Dola za ta yi aiki. Ga INEC ta matsa ta ce cikin sati guda kowane ya fito da mataimakinsa.
Gaba kura, baya siyaki. Ni Tinubu! Ina zan sa kai na?
In da kai ne Tinubu, ya za ka yi?
Dr. Aliyu U. Tilde
10 Yuni 2022
Discussion about this post