Kwararren masani kuma mai sharhi kan al’amuran siya tsohon shugaban Cibiyar Nazarin Harkokin Dimukraɗaiyya ta Manbayya House, Habu Muhammad, ya bayyana ziyara da ɗan takarar shugabancin ƙasar nan a ƙarƙashin tutur jam’iyyar APC Bola Tinubu, a matsayin wani ɓangare na son gadar buzun shugaban ƙasa Muhammad Buhari, a kakar zaɓen shekara ta 2023 mai zuwa.
Farfesan Muhammad na tsangayar kimiyyar Siyasa dake Jami’ar Bayero Kano, ya shaidawa PREMIUM TIMES HAUSA cewa ” Tinubu ɗan siyasa ne da ya yarda da cewa matuƙar ya samu goyon bayan jihohin Arewa, irin su Kano to babu shakka mafarkin sa na zama shugaban ƙasar Najeriya, zai zamo gaske.
A cewar sa kaso biyu cikin uku na masu kaɗa ƙuri’a a Arewacin Najeriya sun fito ne daga Jihar Kano, wanda hakanne ya sanya shi shirya babban taron sa kashi na 12 a jihar a matsayin wani ɓangaren na neman tsayawa takarar 2023.
Sai dai da dama daga cikin mutane na iƙirarin cewar zagayen da Tinubu, ya ke yi a yankin na arewa wata hanya ce samar da haɗin kan yankin.
Ya ce da wannan zagayen da ya ke zaifiye masa da ya tara manyan jagororin yankin Kudu, domin sanar da su manufar sa ta tsayawa takara a kakar zaɓen shekara ta 2023.
Har wa yau Farfesan ya ce tsohon gwamnan jihar Legos, na da ƙalubale babba da zai fuskanta a yankin arewa matuƙar al’ummar yakin na ci gaba da ganin yadda jama’a ke kallon irin yadda Hausawa da Fulani ke ci gaba da rasa rayukan su da ma faɗan manoma.
Dai dai da sau ɗaya Tinubu bai taɓa tsoma bakinsa kan irin rikicin dake faruwa a yankin kudan cin ƙasar nan, musamman yadda ‘yan kasuwar da suka fito daga arewa ke cikin gaba da fuskantar barana wani lokacin har da kai musu hari.
Ya ce matuƙar ya zuba ido hakan su ka ci gaba da faruwa to kwa ba makawa tasirinsa a arewacin Najeriya, zai gaza kai bantansa.
A cewar sa idan muka kalli siyasar Kano, musamman babban ƙalubalen da ke gaban Jam’iyyar NNPP da kuma rashin iya tafikantar da jagoranci a ƙarƙashin mulkin Ganduje.
Sanin kowa ne Kano, itace jiha mafi shahara a arewacin Najeriya, haka kuma itace alƙiblar siyasar yankin, wanda ko a babban zaɓen shekara ta 2015 jam’iyyar APC ta tsira da ƙuri’u kimanin miliyan 1 da dubu ɗari 9, haka a shekara ta 2019 jam’iyyar ta tsira da makamanciyar haka.
A wani bincike da PREMIUM TIMES HAUSA tayi ya bayyana cewa ɗan takarar Shugaban ƙasa a jam’iyyar ta APC, Tinubu ya daɗe yana tsare tsaren sa har ma da samun damar haɗuwa da wasu masu karfin faɗa aji a jihar da mutanen cikinta ke ƙaunar jam’iyyar.
To sai dai magana ta gaskiya jam’iyyar APC, a Kano, bata da wani karsashi duna da yadda gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya yiwa jam’iyyar kisan mumuƙe ya yi da yake gudanar da salon mulkinsa.
Ganduje a jihar Kano, ya yi sanadiyar barin wasu daga cikin jiga jigan jam’iyyar ɗauke da fishin abinda aka yi musu da su ka haɗar tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, maitaimakawa shugaban ƙasa Muhammad Buhari, kan harkokin majalisa Kawu Sumaila, inda suka koma jam’iyyar NNPP, wanda kuma hakan ana ganin zai yiwa ɗan takarar giɓi wajen samun ƙuri’un da yake tsammanin.
Idan aka haɗa jiga-jigan da su ka haɗa da Kawu Sumaila, da Jibrin Kofa da suka fito daga yankin Kano ta Kudu wacce take da kimanin mazaɓu 15, wanda ko a iya ƙaramar hukumar Rano kawai akwai kimanin mutum 71,641 duk da har zuwa yanzu INEC bata fitar da adadin jama’ar da sukayi rijistar zaben wannan shekarar ba.
A Don haka jam’iyyar APC yankin Kano ta Kudu na da babban ƙalubale da a gabanta a babban zaɓe mai zuwa duk da cewa bulaliyar Majalisan wakilai maiwakiltar Tudun-wada da Doguwa Alhassan Ado, ya yi iƙirarin cin nasarar jam’iyyar kamar yadda aka gani a baya.
To sai dai a yankin Kano ta arewa da ke ɗauke da mazaɓu 14 wadda Sanata, Barau Jibril ke wakilta na da yaƙinin irin nasarorin da su ka cimma a yankin jam’iyyar za ta taɓuka abin arziki duba da a yankin sirikin Buhari ya fito wato Sarkin Bichi Nasiru Ado Bayero.
Arewa Maso Yamma
Idan muka duba Kano ta tsakiya kuwa jam’iyyar APC zata fuskanci manya manyan jagororin yankin wato Sanata Malam Ibrahim Shekarau da Kwankwaso da suka fito daga jam’iyyar NNPP wanda sanin kowa ne tsihon gwamna Kwankwaso na da ɗibum magoya baya a jihar Kano, haka ma Malam Shekarau.
Haka zalika akwai wasu rikice rikicen cikin gida da jam’iyyar ke fuskanta a wasu yankunan da ke cikin ƙwaryar nirnin Kano, tun bayan zaɓen fidda gwani da jam’iyyar ta yi wanda harzuwa yanzu ake zaman doya da manja a tsakanin wasu ‘ya’yan jam’iyyar da aka kasa sasantawa.
Yayin da wasu ɗinbum magoya bayan APC ke ganin gazawar gwamnatin tarayya kan abubuwan da su ka tsammaci za su gani a mulkin cikin shekaru 7 da ta shafe tana mulkar wannan jihar.
Duba da wannan hasashe za a iya cewa jam’iyyar NNPP zata iya samun nasarar cin zaɓe a jihar Kano, za kuma ta zamo wake ɗaya mai ɓata gari tsakanin ‘yan takar karun APC da kuma PDP wajen samarwa da Kwankwaso, kaso mai tsoka na ƙuri’un jama’ar yankin.
A arewa maso yammacin ƙasar nan za a iya cewa abun ya sha banban domin kuwa a jihohi irin su Kaduna da Katsina jam’iyyar APC zata ci gaba da riƙe madafun iko duba da nasarorin da gwamnonin yankin su ka cimma duk da cewa akwai ƙalubalen tsaro da jihohin ke fuskanta .
A jihohi irin su Sokoto da Kebbi kuwa za a iya cewa jam’iyyun na da ƙalubale a gabansu wajen cin zaɓen a jihohin.
Arewa ta Tsakiya
Jam’iyyar APC a arewa ta tsakiya kuwa hasashe na nuna cewa a jihar Niger, zata iya samun nasara duba da yadda jam’iyyar adawa ta PDP a ke gani a jihar ta rasa karsashi.
Tun lokacin da aka jiyo tsahon gwamnan Jihar Baban gida Aliyu, ya yi alƙawarin samar da shugabanci a jam’iyyar wanda alokaci guda aka jiyi rashin amon sa sakamakon zargin sa da almundahana.
Jam’iyyar APC da jihohin da take mulki
Jam’iyyar APC a arewacin ƙasar nan na da iko da jihohi 13 cikin 19, ciki kuwa akwai jihohi 3 da suka zamo ‘yan APC gargajiya wato Yobe, Borno da kuma jihar Zamfara, wanda akwai ya ƙinin jam’iyyar PDP ba zata iya cin koda kujerar gwamna a waɗannan jihohi, hankali kwanci Tinubu zai ci zaɓe a jihohin.
Cewar wani ɗan jarida dake zaune babban birnin jihar Yabe, Damaturu ” Jihar Yobe, jiha ce da jam’iya ɗayace kaɗai ke mulkarta domin basu da abokanan adawa, domin na ɗauki tsawon lokaci ina son tantance waye shugaban jam’iyyar PDP a jihar, domin naga bashi da buƙatar tsoma baki a wasu al’amuran da suka shafi jam’iyyar adawa ta APC”.
Ɗan jaridar da ya nemi a sakaye sunan sa domin gudun maganganun sanrai ya ce tun a baya a cewar gwamna Mai-Mala Buni, ya yi alƙawarin maida jihar Yobe, jiha ɗaya da jam’iyar siyasa ɗaya ce zata mulkesu kuma ana ganin haƙan nasa yana cimma ruwa, domun kuwa ba afiya ganin ‘ya’yan jam’iyyar PDP ba har sai lokutan zaɓe.
To sai dai ana ganin ɗan takarar shugaban ƙasar zai girbi abinda gwamnonin jihar Jigawa da Kebbi, su ka shuka na irin zunuban da suka a jihohin nasu, gwamnonin na shan suka kan yadda su kayi babakere, da lalata jihohi nasu ta hanya san rai da wasu buƙatu na ƙashin kansu.
A jihar Jigawa, kuwa ɗaya daga cikin shugabannin jam’iyyar Labour Party Abdullahi Tsoho, cewa ya yi sama da shekaru 7 kenan da aka samu malamai kimanin dubu 9 da kammala wa’adin ayyukan su na gwamnati, amma har zuwa yanzu ba a mayar da wannan gurbin ba.
Mai makon hakan gwamnan ya maida hankali wajen gida ɗakin karatun yaran ba tare da malaman da za su koya musu ba, a cewar Malam Tsoho.
Haka su kansu ‘ya’yan jam’iyyar ta APC a jihar Jigawa, na zargin cewa Badaru da rashin samar da tallafin kayayyakin aikin noma da ake shugowa da su ta ƙasar Sin wato China, wanda farashin kayayyakin aikin noma yafi sauƙi fiya fiye da ka siya a kamfanin da aka ware.
Lamarin da a jihar Kebbi ya tilastawa ‘ya’yan jam’iyyar APC canza sheka zuwa PDP, inda a jigawa kuma lamarin ya sha ban-ban domin kuwa ‘ya’yan jam’iyyar APC ƙin canza sheƙar su kayi tare da tsayawa a jam’iyyar suna jiran ramako ga abida akayi musu.
Inda a yanzu haka gwamnan ke fuskantar Shari’a daga Shugaban jam’iyyar na jihar kuma tsohon ɗan majalisa Faruk Aliyu, kan zargin gwamnan da ƙaƙaba musu ɗan takara dai zaiwa jam’iyyar APC takara wanda su ke ganin hakan a matsayin abinda ya saɓawa dokokin zaɓe.
Rikicin da ake gani ka iya taɓa jam’iyyar APC a babban zaɓen da ke tafe a shekarar 2023.
A arewa masu yammacin ƙasar nan kuwa ana ganin siyasa kan-kan-kan za ayi wato raba dai-dai.
A hasashen irin na su Farfesa Umaru Ibrahim, na tsangayar kimiyyar Siyasa dake Jami’ar Maiduguri, kuwa cewa ya yi da alamu jam’iya mai mulki ta APC za ta iya lashe jihohi 3 cikin 6 a arewa maso yamma.
Fafesan ya shaidawa jaridar Premium Times cewa abu ne mai wahala PDP tayi nasara a jihohin Borno da Yobe har ma da jihar Gombe da jam’iyyar APC ke mulki, don haka Tinubu zai iya sanya jihohin cikin wanda zai yi nasara.
Masanin ya yi tambihi irin na siyasa inda ya ce kasan cewar Atiku Abubakar ya fito daga arewa maso yamma dake da jihohi 6 a yankin, abin baƙin ciki ga Atiku shi ne, jam’iyyar APC mai mulki na da madafun iko a jihar Borno, Yobe da kuma Gombe, inda PDP ke da Jihohin Adamawa, Taraba da kuma Bauchi.
Ya ce APC zata fi karɓuwa a yankin arewa maso yamma matuƙar ta ɗakko mataimakin shugaban ƙasa a yankin.
A Bauchi kuwa malamin ya ce Atiku na da ɗunbin magoya baya wanda hakan zai zamarwa Tinubu wani wani tarnaƙi na samun nasara a jihar.
Batun Takarar Musulmi da Musulmi a Jam’iyyar APC
Shahararren malami kuma mai sharhi kan al’amuran siyasa a ƙasar nan Dakta Sa’idu Dukawa na jami’ar Bayero Kano, cewa yayi yawan ce-ce-kucen da ake tayi na takarar Musulmi da Musulmi ka iya taimakawa jam’iya mai mulki ta APC a wasu daga cikin jihohin arewacin Najeriya.
Zaɓar mataimaki da Tinubu zaiyi nada matuƙar tasiri a tsarin zaɓen da za agudanar domin kuwa zai iya samun ƙuri’u da dama daga jihar Kano da sauran jihohin arewa kamar yadda ya shaidawa Premium Times.
Ya ce ” mu ɗauka cewa Tinubu ya zaɓo musulmi a matsayin mataimaki daga yankin arewa, hakan kaɗai ka iya bashi damar lashe zaɓe a yankunan da jam’iyyar APC ke mulki har ma da ƙarin wasu, idan kuwa zaɓin nasa aka samu akasin haka to kwa lashakka APC za ta rasa wasu daga cikin jihohi domin addini na da tasiri wajen zaɓe.
Dukawa ya ce ko da irin Karaye kiraye-kirayen da shugabannin addinai da sauran ƙungiyoyi su kayi na kada Tinubu, ya sake ya zaɓi Musulmi a matsayin mataimaki na ƙara masa wani ƙaimi da ya fahimci irin mamayar da Musulmi su kayi da shahararsu a yankin arewa.
Lissafin da idan aka duba jihohin 19 dake arewacin Najeriya, jihohi 3 ne Kiristoci ke mulka, wanda kuma kowa ya shaida cewa yawan musulmai a arewa zai sa su so ganin ɗaya daga cikin su aka bawa muƙamin mataimakin shugaban ƙasa.
To sai da a cewar sa wannan tsari zai sanya mafi yawancins kiristocin da ke ƙasar nan ba zasu zaɓi jam’iyyar APC ba a arewacin Najeriya har ma da kuduncinta.
Masanin ya ce dukkanin wani buri ko bukata da jam’iyya itace taci zaɓe, kuma ko da yaushe burin ɗan siyasa shi ne ya samar da wata mafita da zata sanya shi ya ci zaɓe.
A ƙarshe Dukawa ya ce abin da ya kamata ga waɗan da za suyi zaɓe shi ne su tsaya su dubi cancanta ba son rai ba, su zaɓi wanda zai kawo karshen matsalolin tsaro, farfaɗo da tattalin arziƙi ba tare da la’kari da ina ya fito ba ko addinin sa
Discussion about this post