Gungun waɗansu ‘yan bindiga sun afka wa garin Zugu da ke cikin Ƙaramar Hukumar Bukkuyum, su ka banka wa ofishin ‘yan sanda wuta, kuma suka kwashe kayan mutane.
Maharan sun dira garin Zugu wanda shi ne na biyu mafi girma a Ƙaramar Hukumar Bukkuyum, kuma su ka kwashe kaya a wasu gidaje, sannan su ka kwashi kayan abinci da kayan masarufi a wasu kantina.
Shugaban Matasan Bukkuyum Abubakar Garba, ya shaida wa wakilin mu cewa an kai harin ne a ranar Alhamis, wanda sakamakon harin ya sa jama’ar garin kowa ya fashe, ana gudu zuwa cikin Bukkuyum da sauran garuruwan da ke cikin Ƙaramar Hukumar Gummi.
“Maharan sun shuga Zugu ne daga cikin Dajin Ganɗo. An shaida min cewa har sun wuce garin, kuma sai suka koma su ka banka wuta kan ofishin ‘yan sanda, su ka saci kayan abinci da kayan masarufi.
“Mazauna garin sun ce maharan sun ƙone ofishin ‘yan sanda ne don kada sai bayan sun yi gaba ‘yan sanda su yi masu kofar-raggo, su cim masu.”
Wani basaraken da ba ya so a ambaci sunan sa, ya shaida wa wakilin mu cewa lokacin da ‘yan bindiga su ka tunkari ofishin ‘yan sanda, duk arcewa su ka yi.
An tuntuɓi Kakakin Yaɗa Labarai na Rundunar ‘Yan Sandan Zamfara, Mohammed Shehu, amma bai amsa kira ba, kuma bai maida amsar saƙon tes da wakilin mu ya tura masa ba.
Discussion about this post