‘Yan ta’addar Boko Haram sun kashe ‘yan jari-bola 55 a hare-hare biyu a Jihar Barno.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Barno Abdu Umar ya bayyana haka lokacin da ya halarci taron masu ruwa da tsaki don wanzar da zaman lafiya a jihar, wanda aka yi a Maiduguri, a ranar Asabar.
Taron dai ya ƙunshi ‘yan sanda, sojoji, SSS, dogarawan sibil difen da sauran su.
An shirya taron ne domin a samo mafitar yadda za a magance hare-haren da ake kai wa ‘yan jari-bola a wasu yankunan cikin jihar, wadda hare-haren ta’addanci ya kassara.
Kwamishinan’Yan Sanda ya ce Boko Haram sun halaka ‘yan jari-bola 32 a ƙauyen Modu, cikin Ƙaramar Hukumar Kala Balge. Sai kuma wasu 23 a ƙauyen Mukdala cikin Ƙaramar Hukumar Dikwa.
Ya ce sun shiga daji ne neman ƙarafan tsoffin motoci ne har su kayi nisan kilomita 25 daga cikin gari, inda aka can Boko Haram su ka bindige su.
Gwamna Babagana Zulum ya nuna takaicin kisan mutanen 55. Sai dai ya yi ƙorafin masu yin jari bola ke lalata kayan gwamnati irin su motocin gwamnati, su na cire wasu sassan motocin su na sayarwa.
Sai dai kuma Shugaban Ƙungiyar Masu Jari-Bola na jihar, Umar Usman ya ce dukkan waɗanda aka bindige ɗin su 55 ba mambobin su ba ne.
Ya ce mambobin su fiye da 3,000 a faɗin ƙananan hukimomin 23 duk su na da rajistar ƙungiya.
Sannan kuma ya musanta cewa mambobin su na lalata kadarorin gwamnati.
Amma ya yi zargin cewa dukkan waɗanda aka bindige ɗin duk masu zama ne sansanin gudun hijira, waɗanda rayuwa ta yi wa ƙunci a sansanin.