Ɗaya daga cikin ‘yan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC, ya bayyana wa Kwamitin Tantance ‘Yan Takara cewa ba zai taɓa amincewa a janye a bar wa ɗan takara ɗaya ba, sai fa idan shi ne kowa zai janye ya bar masa
John Odigie-Oyegun wanda shi ne Shugaban Kwamitin Tantance ‘Yan Takarar Shugaban Ƙasa na APC, ya shaida wa manema labarai haka a ranar Juma’a, a Abuja.
Ya ce dukkan sauran ‘yan takara 22 sun ce za su amince idan aka cimma matsaya ɗaya, aka tsayar da mutum ɗaya a cikin su, ko ma wane ne.
“Mun tuntuɓi dukkan ‘yan takarar ɗaya bayan ɗaya, a kan maganar fitar da ɗan takara ta hanyar cimma yarjejeniyar amincewa da mutum ɗaya, ba tare da an jefa ƙuri’a a zaɓen fidda gwani ba. Kashi 99 duk sun amince, cewa idan aka tuntuɓi ɓangarori kuma aka cimma daidaito, to sun amince da haka.
“Sai wani ɗan takara ɗaya ne ƙwal ya ce shi ba zai yarda a bar wa kowa takara ba, sai dai idan shi sauran za su bar wa.
“To ina ganin a nan ne zan ƙara jaddada wani abu a kan haka. Wannan ya ba ku ƙarin hasken yadda lamarin ya kai mu ga rage yawan ‘yan takarar.
“To amma a ƙarshe dai, ba tsoron yin zaɓen mu ke yi ba, idan har ta kai mu ga yin hakan ko kuma wani ya ce lallai sai dai a yi zaɓen.” Inji Oyegun.
Oyegun bai faɗi sunan wanda ya ce dai dai idan shi ne za a bai wa ba, amma dai kowa ya san da Bola Tinubu ya ke, wanda a ranar Juma’a ya fito ƙuru-ƙuru ya ce idan dai batun shugabancin Najeriya ake yi a 2023, to a ba shi kawai a huta.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa an zabtare yawan ‘yan takarar da su ka fito a PDP.
An ce waɗanda aka zabtare duk dattawa ne masu shekaru kusan 70 zuwa sama. Lamarin da wasu da dama ke jin cewa lallai akwai sunan Tinubu a cikin waɗanda aka zabtare ɗin.
Kakabin Tinubu Kan 2023: Lokaci Na Ne, A Bani A Huta:
‘Ba don ba da Buhari bai zama Shugaban Ƙasa ba’ -Inji Asiwaju:
Ɗaya daga cikin ‘yan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu, ya bayyana cewa shi ne gogarman da ya cicciɓa Muhammadu Buhari ya zama Shugaban Ƙasa a 2015 da 2019.
Tinubu ya yi wannan furuci a lokacin da ya kai wa Gwamna Dapo Abiodun na Jihar Ogun ziyara, inda har ya gana tare da wakilan zaɓen ‘yan takarar APC na Jihar Ogun.
Ya je ne domin neman goyon bayan wakilan zaɓen ‘yan takara, wato deliget na jihar.
Gorin Da Tinubu Ya Yi Wa Buhari:
“Ba don ni da na tsaya bayan Buhari ba, da bai zama shugaban ƙasa ba.” Haka Tinubu ya furta a wurin.
“Buhari ya jaraba sa’a da farko, bai samu nasara ba. Ya ƙara fitowa takara a karo na biyu, ya sha kaye. Ya fito karo na uku, nan ma ya sha kaye.
“Kai, Buhari fa har kuka ya riƙa rusawa aka nuno shi a talabijin ya na cewa ba zai sake yin takara ba.
“Daga nan na je har Kaduna na same shi, na ce za ka sake yin takara, kuma za ka yi nasara. Amma fa kada ka sake ka raina wa Yarabawa hankali. Ya ce ya amince.
“Tun da Buhari ya hau bai taɓa ba ni alfarmar na ba shi wani ya naɗa minista ba. Buhari bai taɓa ba ni kwangila ba. Ban taɓa roƙon komai a wurin sa ba. To yanzu lokacin da Yarabawa za su yi mulki ne, lokaci na ne.”
Tinubu ya ce shi ne ya ɗaure wa Abiodun gindi har ya zama Gwamna kuma shi ne silar zaman Osinbajo Mataimakin Shugaban Ƙasa.
Shi dai Dapo Abiodun ya nuna goyon bayan sa ne ga Yemi Osinbajo, ɗan asalin Jihar Ogun, wanda shi ma Osinbajo ɗin ya fito takara.
“Shi kan sa Gwamnan ga shi nan zaune, idan ba don Allah da kuma taimako na ba, da bai zama Gwamna a nan Jihar Ogun ba.” Inji Tinubu.
Tinubu ya kuma bada labarin yadda aka ƙi ɗaukar sa ya zama Mataimakin Shugaban Ƙasa a 2015, saboda wai shi Musulmi ne, kamar Buhari. Amma sai ya bada sunan Yemi Osinbajo, ya ce a ɗauke shi.
Sannan kuma ya tunatar da yadda Atiku ya garzaya ya same shi, aka ba shi takarar shugaban ƙasa a AC, haka shi ma Nuhu Ribadu aka ba shi takara a ACN.
Tinubu ya nemi wakilan zaɓe su zaɓe shi domin ya fi sauran cancanta.
Discussion about this post