Waɗansu daga cikin Sanatoci 58 da ba za su koma Majalisar Dattawa a zaɓen 2023 ba, sun fara shan raɗaɗin zafin tunanin barin katafaren zauren da su ke zama su na kafa dokar ƙasa, bijiro da ƙudirori da kuma lale katin kasafin kuɗaɗe.
A cikin 58 ɗin nan, wasu sun ci taliyar ƙarshe kenan ba za su sake komawa ba. Wasu kuma sun kai wa’adin ƙarshen alewa ƙasa, wato idan sun bar Majalisar jin daɗin mulki kuma ya ƙare, sai dai mulkin matan su, ‘ya’yan su da direbobin su.
Akwai kuma waɗanda ko da za su shekara 20 bayan tsame su a cikin tandun mai, jikin su ba zai daina tsatstsafo naso, danshi da maiƙo ba. Irin su ne ke daɗewa su na cin tulin kuɗaɗen da su ka tara da kuma waɗanda su ka raruma.
Dattawan cikin su da su ka maida majalisar wani dandalin zuwa a riƙa sharar barci har da minshari kuwa, yanzu alƙiyamar zaman na su a can ta tashi, sai dai su koma gida su ci gaba da barci, yaran gida kuma na damun su da hayaniya a cikin kunnuwa.
Cikin waɗannan Sanatoci 58 da ba za su koma Majalisar Dattawa ba, akwai waɗanda su ka yi rantse su ka saki hanya, su ka taka ƙaya. Wasu da su ka ratse kuma sartse su ka yi. Kai, wasu ma ‘majici ne ya sare su’, har a kai ga sake sabon zaɓe su na kwance.
PREMIUM TIMES Hausa ta bi diddigin waɗannan Sanatoci domin ƙoƙarin warware dalilan da ya sa wasu da dama a cikin su ba za su koma ba.
Sanata Abdullahi Adamu wanda ya sauka aka ba shi muƙamin Shugaban APC na Ƙasa, ba zai koma Majalisar Dattawa a zaɓen 2023 ba. Ga alama ma shi da Majalisar sai dai a ce ‘haihata-haihata’, domin a yanzu dai shekarun sa 75 a duniya. Idan da rai da lafiya kuwa, a zaɓen 2027 zai kasance Adamu na da shekaru 80.
A halin yanzu akwai irin su Sanata Ahmad Lawan, Ike Ekweremadu da Nicholas Mutu da su ka shafe wajen shekaru 20 a Majalisar Dattawa. Ko da ya ke a Amurka akwai wasu sanatocin da su ka shafe har shekaru 30 a Majalisar Dattawa.
A Najeriya, wani rahoto da cibiiyar NILDS, wato Cibiyar Nazarin Majalisu da Dimokraɗiyya ta wallafa cikin 2015, ya Sanata 27 ne daga cikin 109 su ka sake komawa Majalisar Dattawa. A zaɓen 20011 kuwa 35 kaɗai aka sake zaɓe.
A Majalisar Tarayya kuwa, Mambobi 108 daga cikin 360 su ka sake cin zaɓe a 2003. Guda 110 a 2007, sai kuma 103 a 2011.
Mene Ne Dalili?:
Da farko ana ganin sabbin-yanka-raken sanatoci ba su cika komawa ba, saboda idan su ka shiga, su kan kwashe shekaru biyu kafin su goge har a riƙa damawa da su ko kuma a riƙa tsula tsiya tare da su.
To kafin su kai ga samun zaman da za su yi wa jama’a aiki, zaɓe ya zo har an yi ‘waje rod’ da su.
Zaɓen 2023: Aƙalla dai akwai Sanatoci 58 daga cikin 109 da ba su koma Majalisar Dattawa ba. Wasu a zaɓen fidda gwani aka kayar da su, wasu kuma bayan sun sha kaye, sun rungumi wata jam’iyyar da ko a can da wahala su iya kai labari.
Dalilan rashin komawar da yawa daga cikin su na da nasaba da rikicin siyasa da gwamnonin jihohin su.
Da yake gwamnoni ke da wuƙa da nama a kowace jiha, duk Sanatan da ya yi faɗa da Gwamna zai iya rasa kujerar takarar sa.
An ga haka kan Adamu Aliero, Babba Kaita da sauran su da dama.
Wasu kuma ba za su koma ba saboda sun tafi takarar gwamna ne a zaɓen 2023. To su waɗannan idan sun ci zaɓe ba za su koma Majalisar Dattawa ba. Idan ma ba su ci zaɓen ba, gida za su koma su huta sannan su sake shirin wani zaɓen a 2027.
Akwai kuma waɗanda ba za su koma Majalisar Dattawa ba, saboda sun shiga takarar shugaban ƙasa, ba su yi nasara ba, kuma ba su yi zaɓen fidda gwani na takarar sanata ba. Wato irin su Ahmad Lawan, Godswill Akpabio da sauran su.
Sunayen Sanatoci 58 Da Su Ka Yi Wa Majalisar Dattawa Cin-taliyar-ƙarshe:
Akwai kuma Ibikunle Amosun, Ajayi Borroffice, Rochas Okorocha.
Waɗanda su ka tafi takarar gwamna a cikin Sanatoci sun haɗa da Ovie Omo-Agege, Emmanual Bwacha, Uba Sani, Aishatu Ɗahiru, Teslim Folarin, Sunday Onor da kuma Sanata Chukwuka Utazi na Enugu, wanda ya amince ba zai koma takara ba, ya ba Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi damar maye gurbin sa a bisa yarjejeniya.
Akwai kuma Sanatocin da ba za su koma ba, saboda yarjejeniyar yin karɓa-karɓar takarar sanata tsakanin ƙananan hukumomin da sanata ke wakilta.
Akwai waɗanda su ka yi ritaya don ƙashin kan su, kamar Nora Daduut ta Jihar Filato da Theodore Orji na Jihar Abia da kuma Oluremi Tinubu ta Jihar Legas.
Nora shekarun ta uku kacal. Ita ce aka zaɓa bayan mutuwar Ignatius Longjan.
Sanata Theodore Orji kuwa alƙawari ya yi kuma zai cika cewa, zai yi ritaya daga siyasa cikin 2023.
Sauran Sanatocin Da Ba Za Su Koma Majalisa Ba:
Akwai Dinka Hezekiah, Gyang Istifanus, Smart Adeyemi, Yakubu Oseni, Sabi Abdullahi, Godiya Akwashiki, Ibrahim Oloriegbe, Orker-Jev Emmanual, Yusuf Yusuf da Amos Bulus.
Sai kuma Ayo Akinuelure, NicholasTofowomo, Tolu Odebiyi, Mathew Urhoghide, Gershom Bassey, James Manager, George Sekibo, Betty Apiafi, Albert Bassey da Chris Ekpenyong.
Akwai kuma Rochas Okorocha, Ibrahim Hadejia, Danladi Sankara, Mohammed Nakudu, Bello Mandiya, Kabir Barkiya, Lawali Anka, Danjuma La’ah, Victor Umeh, Moses Cleopas, Mohammed Bulkachuwa da Chukwuka Utazi.
Sanatoci 7 Da Su Ka Canja Sheƙa Su Ka Tsaya Takara a Wata Jam’iyya:
Adamu Aliero, Babba Kaita, Francis Alimekhena, Enyinnaya Abaribe, Francis Onyewuchi, Ibrahim Shekarau da Lawan Gumau.
Discussion about this post