Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AAC, Yele Sowore ya bayyana Abubakar Magashi ɗan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar AAC.
Jam’iyyar AAC ta zabi mawallafin jaridar Sahara reporters a matsayin ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a gangamin jam’iyyar da ta a Abuja a watan jiya.
Da yake bayyana Abubakar Magashi ga manema labarai, Sowore ya ce Magashi na da karfi irin na siyasa da zai iya lashe wa AAC kuri’un jihar Kano kaf.
” Yanzu dole ƴan siyasa irin su Kwankwaso su shiga taitayin su, zuciyar su ta rika bugawa da gudun tsiya don ko ɗan takarar mataimakin shugaban kasa da muka zaɓa, Magashi dodon su ne.
” Magashi zai kawo mana ƙuri’un jihar Kano kaf, su Kwankwaso za su ji a salansa ne, saboda ya fi su soyiwa a idanun mutane sannan ya fisu kafuwa a siyasance a Kano.
Discussion about this post