DUBAWA ta bi diddigin bayanai da hotuna da ake ta yadawa a kafafen yada labarai da na yanar gizo cewa wai gwamnonin Arewa sun ziyarci dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar bayan yayi nasara a zaben fidda gwani.
Bidiyon wanda ya karade shafukan kafafen sada zumunta a yanar gizo ya sa mutane da dama na tofa labarkacin bakin su akai.
Sai dai kuma binciken da DUBAWA ta yi mai zurfin gaske, inda ta bi diddigin gaskiyar maganar ya nuna cewa wannan magana ba haka ya ke ba.
” Gwamnoni sun yi kiciɓus da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a gidan Ɗahiru Mangal ne wajen yin ta’aziyya tun a watan Janairu.
Atiku da kansa ya saka a shafin sa ta tiwita cewa a wannan rana ya ziyarci Ɗahiru Mangal domin yi masa ta’aziyyar rasuwa da aka yi masa.
A wannan rana gwamnonin APC na yankin Arewa suma sun kai Irin wannan ziyara gidan Mangal.
Bincike dai ya nuna cewa ba gaskiya bane wai bayan nasarar da Atiku ya samu a zaɓen fidda gwani gwamnoni sun yi tattaki ta musamman zuwa gidan sa domin taya sa murna.
Wannan bidiyo da hotuna sun karaɗe shafukan yanar gizo har wasu da dama suna ta tofin Allah kyauta da kuma nuna mamaki a kau.