Tsohon gwamnan jihar Barno, Sanata Kashim Shettima ya nemi afuwar mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da Ahmed Lawan bisa kalaman da yayi a akan su a lokacin da yake hira da talbijin ɗin Channels a cikin makon jiya.
A hirar Shettima ya ƙalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari da kada ya kuskura ya zaɓi wani da ba tsohon gwamnan jihar Legas ba, Bola Tinubu ɗan takarar shugaban kasa.
Shettima ya ce ba maganan takara kawai ake yi ba, maganan wanda zai iya fafatawa da Atiku ake yi.
” Idan ka ce Ahmed Lawan, wa ya san Ahmed Lawan a Najeriya, idan katafi yankin kudu, irin Ohifia ka tambayi mutane wanene Ahmed Lawan, za su yi zaton wani mai tallan Timatir ne daga Maiduguri. Ba a san shi ba.
” Ni na mara masa baya ya zama shugaban majalisar dattawa duk da ɗan jiha ta Ali Ndume ya fito nema. Ahmed Lawan ya ci zaɓe da ƙuri’u da ƙuri’u akalla 144,000 ne, ni ko na ci zaɓe da kusan ninkin kuri’un sa sau uku.
” Shi ko mataimakin shugaban Kasa Yemi Osinbajo, mutumin kirki ne mai hakurin gaske. Amma irin su Osinbajo siyar da Ice Cream da Gugguru ne ya fi dacewa da shi, amma ba shugabancin cukurkuɗaɗɗiyae kasa irin Najeria ba.
” Tinubu ba sabon ɗan siyasa ba ne, ya goge kuma babu wanda inda a sanshi a faɗin kasar nan ba. Kuma shine zai iya fafatawa da Atiku kafaɗa da kafaɗa a kada shi.
” Inda giwaye ke shawagi, ba wuri ne na wasan ƙadangaru da kiyashi ba, Tinubu giwa ne, sauran kuwa duk kiyashi ne, murƙushe su zai yi.
Sai dai kuma Shettima ya roki afuwar mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da shugaban majalisar Dattawa Ahmed Lawan.
” Na yi waɗannan kalamai ba don in ci mutuncin su ba ne. Na yi ne don kawai in nuna wa mutane cewa Tinubu na gaba da kowa ni ɗan takara a wannan jam’iyya, kuma shine ya kamata a zaɓa wanda zai cira tutar APC a zaɓen da ke tafe.