Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ya bayyana cewa zaɓen Bola Tinubu ɗan takarar APC a zaɓen 2023 ya nuna tabbacin cewa jam’iyyar ta su ce za ta yi nasara.
A cikin wasiƙar da Lawan ya aika wa Tinubu a ranar Laraba, bayan Tinubu ɗin ya kayar da shi a wurin zaɓen fidda-gwani, Shugaban Majalisar Dattawa ya ce Tinubu ne wanda ‘yan APC su ka fi so ya tsaya masu takara.
Daga nan kuma Lawan wanda ya samu ƙuri’u 152 kacal, ya bayyana wa Tinubu dalilin da ya sa ya yi takara tare da shi.
“Kamar yadda Mai Girma Tinubu ya sani, na fito takara ne inda na yi gogayyar haɗa kafaɗa da irin ku masu ƙwarewa, don ni ma na bayar da tawa gudummawar, a wannan mawuyacin hali da mu ke a ciki.
Tuni dai ake ta taya Tinubu murnar lashe zaɓe, inda jama’a su ka yi ta murna a Legas.
PREMIUM TIMES Hausa ba buga labarin cewa Atiku Abubakar ɗan takarar PDP ya taya Tinubu murnar zama ɗan takarar APC na zaɓen shugaban ƙasa da za a yi cikin 2023.
Atiku ya taya Tinubu murnar lashe zaɓen fidda-gwanin APC, ya ce Asiwaju ya ci gudu shi ya sa ya kama zomon.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na zaɓen 2023 mai zuwa a ƙarƙashin PDP, Atiku Abubakar, ya taya Bola Tinubu murnar lashe zaɓen fidda-gwanin APC da ya yi.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin sa na Twitter, Atiku ya ce ba a banza Tinubu ya yi nasara, sai da ya ci kwakwar gwagwarmaya sosai.
“Ina taya ka murnar lashe zaɓen fidda gwani na APC. Ka sha fama kuma ka samu nasara, bayan jajircewar da ka yi.” Inji Atiku.
Tinubu ya kayar da ‘yan takara 14 sannan ya zama ɗan takarar jam’iyya mai mulki a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 da ke tafe.
Ya samu ƙuri’u 1,271, Rotimi Amaechi ya samu 316, kuma ya zo na biyu, sai Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo ya zo na uku da ƙuri’u 235.
Bakwai daga cikin ‘yan takarar dai sun janye tare da nuna goyon bayan su ga Tinubu, tun kafin ma a fara jefa ƙuri’a.
Makonni biyu da su ka gabata Tinubu ya taya Atiku murnar lashe zaɓen fidda gwani na PDP. Kuma ya yi fatan cewa Allah ya sa su biyun ne za su yi karon-battar neman zama shugaban ƙasa a zaɓen 2023.