Awowi kadan bayan ficewar sa daga jam’iyyar APC, sanata Adamu Aliero yayi nasara a zaben fidda dan takarar sanatan Kebbi ta tsakiya.
Aliero ya kada Haruna Sa’idu-Dan-diyo da ya samu kuri’u 15 inda shi kuma ya samu kuri’u 246.
Kebbi ta tsakiya ta kunshi kananan hukumomin Kebbi, Gwandu, Jega, Maiyama, Koko-Bese, Kalgo, Aliero da Bunza
Sanata Adamu Aliero ya bayyana komawarsa PDP daga Jam’iyyar APC ranar Alhamis.
A sanarwar da yayi ranar Alhamis, Aliero ya ce rashin jituwa tsakanin sa da jam’iyyar a jihar ya sa dole ya hakura da jam’iyyar ya koma PDP.
Idan ba a manta ba Jam’iyyar APC ƙarkashin gwamna Abubakar Bagudu ta wancakalar da ɗan takarar gwamnan jihar sanata Abdullahi wanda ke ɓangaren Aliero.
Aliero ya ce ” Na gaji da zaman takaici a APC, ba zan iya cigaba da ɗaukan wulaƙanci, wariya da iko da ake nuna min da magoya baya na ba. A dalilin haka na hakura da jam’iyyar.
Discussion about this post