Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa ta ceto mutum sama da 3,000 daga hannun ‘yan bindiga daga shekarar 2019 zuwa yanzu.
Kwamishinan yada labarai na jihar Ibrahim Dosara ya sanar da haka a garin Gusau da yake jawabi kan cigaban da gwamnatin ta yi a jihar ta samu wajen yaki da yan bindiga.
Dosara ya ce wadannan mutane sun samu kubuta daga hannun mahara a dalilin shirin yin sulhu tsakanin gwamnati da ‘yan bindiga da gwamnatin Bello Matawalle ya tsara shekaru uku da suka gabata.
Ya ce hakan na daga cikin manyan nasarorin da gwamnatin Matawalle ta samu a fannin tsaro a jihar.
“Kafin Matawalle ya hau mulkin jihar Zamfara na fama da hare-haren ‘yan bindiga da yin garkuwa da mutane.
“Da Matawalle ya zama gwamnan jihar ya tsara shirin yin sulhu tsakanin gwamnati da mahara wanda hakan ya haifar wa jihar da abin alkhairi ta hanyar frage matsalar yan bindiga a jihar.
Sulhu tsakanin gwamnati da ‘yan bindiga ya taimaka wajen samun tubabbu ‘yan bindiga da suka ajiye makamai.
Daga nan Dosara ya ce hanyoyi da dama da ke rufe da ba a iya bi saboda ‘yan bindiga a kananan hukumomi 14 a jihar duk sun bude.
Gwamnati ta kuma siya motoci da sauran kayan aiki wa jami’an tsaron jihar domin inganta aiyukan samar da tsaro a jihar.
Gwamnati ta yi kira ga mutane da su hada hannu da ita domin ganin an kawo karshen matsalar rashin tsaro a jihar.
Discussion about this post