Hedikwatar sojojin Najeriya ta sanar da nasarar da ta yi na kama wata mota cike makil da sinadarin haɗa bam, bindigogi, harsasai, rigunan sojoji da takalma.
Kakakin rundunar sojin Najeriya Onyema Nwachukwu ya sanar da haka a Abuja ranar Laraba.
Nwachukwu ya ce dakarun Najeriya sun kama motar kirar Toyota Camry a mai lamba JAL 492 AA a Obudu jihar Cross Rivers.
” Ko da direban motar ya isa shingen sojoji dake sintiri sai ya wuce kai tsaye ba tare da ya tsaya an duba shi ba, a dalilin haka yasa sojoji suka buɗe wa motar wuta da hakan ya sa dole ta tsaya.
An kama sinadaran hada bam, kayan sojoji, harsasai da sauran su.