Ƙarin wasu ‘yan takara bakwai sun bi sahun Gwamna Yahaya Bello, inda su ma su ka yi fatali da jerin sunayen ‘yan takara biyar da Gwamnonin APC da Kwamitin Gudanarwa su ka miƙa wa Shugaba Muhammadu Buhari.
Sun yi wannan sanarwa ce bayan shi ma Gwamna Yahaya Bello ya yi barazanar cewa ba zai janye daga takara ba. Kuma ya ce idan aka cire sunan sa a jerin ‘yan takara, zai ragargaza APC, ta-ɓare kowa ya rasa.
‘Yan takarar bakwai su ne Ogbonnaya Onu, Gwamna Ben Ayade, Emeka Nwajiuba, Imo, Rochas Okorocha da Tein Jack-Rich.
Cikin wata sanarwa da ‘yan takarar bakwai su ka fitar a ranar Talata, sun ce sunayen da Gwamnonin da Kwamitin Gudanarwa su ka bayar “wasan yara ne kawai.”
Sun ce abin da Gwamnonin su ka yi, wani yunƙuri ne don su ware yankin Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu, saboda babu wanda ya tuntuɓe su kafin a ɗauki wannan matsayar.
Shi ma Gwamna Yahaya Bello ya ce ba zai janye daga takara ba, zan ragargaza APC idan aka cire suna na -Yahaya Bello
Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ya fusata, tare da cewa ba zai janye daga takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC ba.
Bello ya shaida wa manema labarai haka bayan ganawar sa da Shugaba Muhammadu Buhari.
Ya nanata cewa shi bai amince ya janye wa ‘yan takarar Kudu ba. Kuma idan aka kuskura aka cire sunan sa a ciki jerin ‘yan takara, “to ina tabbatar maku cewa an kira babban rikici da babbar murya. Saboda zan jefa APC cikin bala’i a ƙasar nan.”
Bello ya fusata ne ganin yadda aka taka wa takarar sa burki, inda Gwamnonin Arewa 13 su ka goyi bayan a miƙa takara ga Kudu.
Su ma Kwamitin Gudanarwar APC su ka amince da haka, inda su ka aika wa Shugaba Buhari sunayen ‘yan takara biyar na Kudu, babu ɗan Arewa ko ɗaya.
A ganawar da Gwamnonin Arewa na APC su ka yi da manema labarai, Gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna ya ce Yahaya Bello ne kaɗai bai amince a bayar da takara ga Kudu ba. Kuma ya na da ‘yancin yin haka, amma dai ra’ayin su ya rinjayi na sa.
Bello ya ce, “ina da dabbacin cewa idan za a yi zaɓe na gaskiya, ni zan lashe zaɓen, idan ba a yi maguɗi ba.
“An shigo da wannan tsari ne don a danne mu da ake ganin mun fito daga ƙananan ƙabilu. To ni a sani cewa mafi rinjaye ne su ke so na fito takara, wato matasan ƙasar nan.
Duk da Bello bai faɗi matakin da zai ɗauka ba idan babu sunan sa a cikin sunayen ‘yan takara, ana ganin cewa kotu zai garzaya bayan zaɓe, tunda Dokar Zaɓe ta haramta cire wani ɗan takara a cikin sunayen waɗanda za a zaɓa.
Discussion about this post