A halin da ake yanzu dai a Arewa za a iya cewa ‘yan takara uku ne za su yi yaƙin buga-in-buga a ranar zaɓen shugaban ƙasa. Akwai Rabi’u Kwankwaso na NNPA, akai Bola Tinubu na APC, akwai kuma Atiku Abubakar na PDP.
Waɗannan ‘yan takara uku ko shakka babu, za su kama alkyabbar Arewa kowa ya sa wuƙa ya yanki iyar yankin da zai iya isar sa yin fatari, wando ko warki a ranar zaɓe.
Idan aka dubi waɗannan ‘yan takara aka yi masu kallon ‘yan dambe, za a fahimci cewa duk irin ƙarfin da su ke da shi, a Arewa ne za a yi yaƙin a ƙare, kuma a kashe na kashewa, wanda ya yi nasara kuma ya sai murna.
Bola Tinubun APC: Zaren damben Bola Tinubu mai ƙwari ne, kuma murɗaɗɗe, yadda kowa ya buga zai iya kai shi ƙasa. Sannan kuma ya na da ƙarfin arzikin da zai sheƙa wa makaɗa da maroƙa kuɗi su yi masa kirari sosai.
Tun a yanzu Tinubu ya nuna cewa ya shirya, domin yaron sa ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Ekiti da ƙuri’u masu rinjayen gaske.
Tinubu na da ƙarfin gwamnonin APC da kuma ƙarfin gwamnatin tarayya. Irin wannan taron-dangi idan su ka yi wa mai ƙaramin ƙarfi, dukan kwaf-ɗaya za su yi masa. Idan kuma mai ƙarfi ne, su yi masa taron-dangi, su yi masa sukan-kabarin-kishiya.
Babbar matsalar da Tinubu zai fuskanta a Arewa ta na da yawan gaske. Na farko dai masu kallon dambe na ganin jikin sa ya saki, ya yi tsufan da ko ya naɗa zaren damben sa ya kai naushi ko kutufo ko ƙulli, ba zai iya kai Atiku ko Kwankwaso a ƙasa ba. Saboda jikin babu ƙwari, ƙafafun ba a dire su ke ba, sannan kuma damtsen babu ƙwanji.
Na biyu kuma shi ne a Kano Kwankwaso ya rigaya ya buwayi lungu da saƙo, ta yadda duk da cewa jam’iyyar sa sabuwa ce, amma shi da ya ke tsohon hannu ne, to ya ƙwace wa APC magoya baya da yawa. Dama kuma na sa magoya ban daga PDP su ka bi shi kamar kaza da ‘ya’ya. Aka bar su Aminu Wali, Mohammed Abacha da Sanata Lado a PDP, tare da mutanen da ba su wuce yawan garken shanun Sarkin Fulani ba.
Abin dubawa shi ne, ƙuri’un jihar Kano sun fi yawan ƙuri’un jihohi bakwai ko kusan takwas ma. Shi ya sa duk wani shahararren ɗan dambe idan bai yi kisa a damben Kano ba, to damben sa bai kai dambe ba.
Idan aka lura da tafiyar APC, za a ga ta fara cikin karo da baƙin jini, kamar yadda aka riƙa yi wa PDP a 2014 da 2015.
Rashin tsaron da ya ƙara dagulewa a Arewa ya kawo wa APC mai mulki baƙin jini a yankin. Har ta kai jama’a da dama su na yin tir da waƙar ‘Jagaba Shi Ne Gaba’, wadda Dauda Kahutu (Rarara) ya yi masa.
Ko da ya ke Tinubu na iya taɓukawa Kano, tunda ya na da manyan mafarauta, irin su Gwamna Ganduje da kuma gwamnatin jihar ɗungururum. Ko da hayagaga za su iya fitar da shi kunya. Sai dai a yi wadda za a yi.
Atiku Abubakar: Matsa Ka Buga ‘Dai Ɗan Sadauki, Tunda Mazaizai Sun Yi Laushi’:
Haka dai mawaƙi marigayi Musa Ɗanƙwairo ya zuga Atiku, wanda a yanzu shi ne Wazirin Adamawa.
Maganar gaskiya duk da ana kallon kamar Atiku ya shirya, to akwai jan aiki a gaban sa. Irin yadda APC ta yagalgala PDP a zaɓen gwamnan Ekiti da aka yi a ranar Asabar, ya nuna PDP ta ɗaura banten kokawa ba ma tukunna.
Yayin da Bola Tinubu ya dira Ado-Ekiti ya na taya ɗan takarar gwamnan APC kamfen, shi Atiku shagaltuwa ya yi da zaman dirshan a Abuja, ya na tarukan da kawai fesa Turanci ake yi, wanda ba ya iya hana iska kayar da mai kayan kara.
A Kano, ƙarfin PDP ya ragu, Kwankwasiyya ko na ce NNPP ta maƙure mata wuya, ta suma. Sannan kuma duk wani masanin siyasa a Kano ya san cewa irin su Aminu Wali da Sanata Lado da Mohammed Abacha ba kalar zubin manyan mafarautan da za su iya ƙwato wa Atiku nama a bakin kura ba ne.
Idan Atiku ya yi wasa, tun da wuri za a tiƙa shi da ƙasa a Kano. Mutumin da Kanawa su ka kayar kuwa babu wani tasirin da zai iya yi ko da a garin su. Abin a jinin siyasar su ke.
Kamata ya yi a ce Atiku ya miƙe kamar da gaske. Ba wai ya tsaya Abuja ya na Turance ‘yan Arewa ba. Dannowa ya kamata ya yi da ƙarfin sa, da jinin sa, da jikin sa. Kai har ma da jakar kuɗin sa. Ko banza dai daliget sun nuna wa duniya cewa sai da kuɗi a ke cin zaɓe a Najeriya.
To mene ne amfanin kuɗin Atiku idan ba za su iya ci masa zaɓe ba?
Rabiu Kwankwaso: Jure Fari Sai Tofa:
Duk irin iya tuggun ɗan siyasa, matsawar adawa ya ke yi da Kwankwaso, to hankalin sa ba ya kwanciya, sai fa ranar da ya ga cewa shi ne ya yi nasara.
Allah ya bai wa Kwsnkwso da tafiyar siyasar ta Kwankwasiyya farin jini. Ba don kuɗi ake son Kwankwaso ba, kuma ba don a samu kuɗi ake bin sa ba. Kauna ce da kuma aƙida irin ta magoya bayan siyasar NEPU da PRP a zamanin marigayi Malam Aminu Kano.
Kwankwaso zai iya zama ‘Kada Dama Ruwa’ a wannan zaɓen. Zai iya gurgunta masu ƙafafu a Kano da wasu jihohi, musamman ganin yadda a kullum jam’iyyar sa ke ƙara cika dalilin yadda hasalallun ‘yan takarar da aka ɓata wa rai a APC da PDP ke tururuwar shiga jam’iyyar sa ta NNPP, mai kayan marmari.