Rahotanni sun tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon Sakataren Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa (NFF), Sani Toro.
An yi garkuwa da shi ne a ranar Asabar, tare da tsohon Mataimakin Kociyan Super Eagles, Garba Yila.
An kama su ne kan hanyar Akwanga, lokacin da su ke kan hanyar komawa Bauchi daga Abuja, bayan sun halarci daurin auren ɗiyar tsohon Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya, Aminu Maigadi.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Bauchi Ahmed Wakili, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce ba shi da cikakken bayani.
“Tabbas wani daga cikin ‘ya’yan sa ya kira ni ya faɗa min cewa an yi garkuwa da baban su kan hanyar Akwanga a Jihar Nasarawa.
“A yanzu dai ba ni da cikakken bayanin, saboda ba a cikin Jihar Bauchi aka yi garkuwar da ba.”
Garkuwa da mutane ta zama ta’addanci a Arewacin ƙasar nan. Tuni ma wasu sun maida ta hanyar samun kuɗi cikin sauƙi.
A yanzu haka akwai ɗaruruwan mutane maza da mata waɗanda ke hannun ‘yan bindiga a cikin dazuka daban-daban na Arewacin ƙasar nan, har ma da Kudu.