Yayin da mafi yawan ‘yan Najeriya ke masa kallon ba ya nuna tausayi da damuwar sa kan mumnunar matsalar tsaro, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana ce “a kullum da takaici da damuwar matsalar tsaro ya ke kwana kuma ya ke yini.
Buhari ya yi wannan bayani a cikin jawabin sa na murnar Ranar Dimokraɗiyya, a ranar Lahadi, 12 Ga Yuni.
“Mu sa waɗanda su ka rasa rayukan su sakamakon hare-haren ta’addanci a cikin addu’a. A kullum ina kwana da tashi da kuma yini cikin tsananin takaici da damuwar matsalar tsaro. Musamman kisan da ake yi wa jama’a da kuma tunanin waɗanda ke hannun ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.
“Sojojin Najeriya na ƙoƙari, amma dai babban abin da aka sa a gaba shi ne a kawo ƙarshen matsalar kuma a kuɓutar da waɗanda ke hannun ‘yan ta’adda baki ɗaya.
A Arewacin Najeriya, Jihar Katsina mahaifar Buhari na a sahun gaban jihohin da matsalar tsaro da dabaibaye. Dubun-bubatar Katsinawa sun tsallake gudun hijira har a cikin Jamhuriyar Nijar.
Jihohin Kaduna, Zamfara, Sokoto, Kebbi da Neja duk sun kasance cikin matsalar tsaro a tsawon shekaru bakwai na mulkin Buharî.
A kusan kullum sai an samu rahoton an yi garkuwa da mutane ko kuma ƴan bindiga sun kashe mutane.