Dan takarar gwamnan jihar Kaduna na jam’iyyar APC, Sanata Uba Sani ya yi sulhu da abokin takarar sa da ya kada a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC Honarabul Sani Shaaban.
Idan ba a manta Sanata Uba Sani ya lallasa Shaaban da kuri’u sama da 1000 in da Sha’aban ya samu kuri’u 16 kacal.
Sai dai kuma bayan zaben, Shaaban ya bayyana cewa bai yarda da sakamakon zaben ba.
Hakan ya sa da yawa daga cikin masu yin sharhi akan zaben fidda gwanin ke ganin akwai sauran rina akaba muddu sanata Uba Sani bai yi sulhu da Shaaban.
Hakan ya sa sanata Uba ranar litinin ya garzaya har gidan Shaaban domin su yi sulhi don cigaban jam’iyyar.
Uba ya ce ” Na tafi gidan Honarabul Sani Shaaban domin mu gana mu kuma tattauna da yin sulhu domin Jam’iyyar mu da zaben dake tafe.
” Shaaban gogagge ne a siyasa, kuma ina tabbatar muku cewa mun tattauna kuma yayi alkawarin lallai za mu yi aiki tare domin ganin jam’iyyar ta yi nasara a zaben gwamna dake tafe.
” Kowa ya san kwarewa da gogewar Honorabul Shaaban. Ya yi alkawarin zai hada hannu da ni kuma zai yi aiki tukuru wajen ganin jama’a sun karkata zuwa ga wannan tafiya don samun nasara a zabe mai zuwa.
Discussion about this post