Shugaban kasa Muhammdu Buhari ya mika sakon taya murnar sa ga Biodun Oyebanji wanda ya yi nasara a zaɓen gwamnan jihar Ekiti wanda ya aka kammala ranar Asabar.
A sakamakon zaɓen wanda aka sanar a garin Ado-Ekiti, 187,057, Segun Oni na SDP ya samu 82,211 sai kuma Bisi Kolawole na PDP da ya samu kuri’u 67, 457.
Buhari ya kara da cewa wannan nasara da APC ta samu nuni cewa har yanzu fa tsinya na nan ɗaure ta mau. Ya yi kira ga ƴan jam’iyyar da a cigaba da aiki tuƙuru da koma haɗin kai a tsakanin juna don min a samu irin wannan nasara a zaɓen 2023 wanda ke tafe.
Idan ba a manta ba, Bola Tinubu ne yayi nasara a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC wanda aka yi a farkon watan Yuni.
Tinubu ya kada sauran ƴan takara da suka haɗa da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, shugaban majalisar Tarayya, Ahmed Lawan , da sauran ƴan takara.