Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu ya bayyana wa manema labarai cewa tuni a ya ɓi wanda zai yi masa takarar shugaban kasa, kuma sunan wanda ya zaɓa na cikin yar takardar sa a gaban aljihu.
” Ƴanci na ne, kuma tuni na zaɓi wanda zai yi min mataimakin shugaban kasa, sunan sa na killace a cikin ƴar takarda ta da na cakale a gaban aljihuna.
Bayan haka Tinubu ya kara da cewa shi mutum ne mai dattaku da sanin ya kamata sannan ya na da kamala da kuma kwarewa a harkar shugabanci da da bunƙasa tattalin arziki.
Aiki ne a gaban mu, Tinubu ga APC
Ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga ƴan jam’iyyar su ɗaura ɗamarar yaki domin jan aiki ne a gaban su.
Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa ranar Alhamis.
Idan ba a manta ba Tinubu ne ya yi nasara a zaɓen fidda gwani na takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC wanda aka yi ranar Litinin zuwa Larabar wannan mako.
Ya lallasa yan takara 14 da suka gobza da shi a zaɓen.
Tsohon ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ne ya zo na biyu a zaɓen inda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya zo na uku a zaben.
Tinubu ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari domin yi masa godiya da damar da ya baiwa duka ƴan takara su gobza a tsakanin su ba tare da ya saka baki ba.
” Ina yin kira ga ƴan jam’iyyar mu ta APC da su zo mu haɗa hannu gaba ɗayan mu domin samun nasara a babban zaɓe.
” Shugaba Muhammadu Buhari ya yi abinda ya dace a wannan zaɓe na fidda gwani. Da ma kuma ya yi alkawarin ba zai sa baki ba a zaɓen kuma ya cika alkawarin sa.
” Yanzu jan aiki ne a gaban mu. Cin babban zaɓe shine ya kamata mu maida hankali a kai yanzu.
Discussion about this post