Na dade ina nazarin yadda gwamnatin gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ta ke gudanar da mulki a jihar Kaduna tun daga 2015 har zuwa yanzu. Babban abinda na gane a ciki shine da farko mutanen jihar basu fahimci irin salon mulkin ba amma kuma a hankali sai suka gane cewa mulki ne na jama’a sannan na talakawa.
Yanzu lokaci yayi da za a mulki zai canja hannu, kuma na kusa da El-rufai wato sanata Uba Sani ne dan takarar APC wanda zai fafata da Honarabul Isah Ashiru na PDP da sauran ‘yan takara. dama kuma a baya El-rufai ya taba cewa wanda zai gaje shi zai fishi nesa ba kusa ba. Wannan ya sa mutane da dama ke ganin zabin Uba Sani yayi daidai ko domin yan Kaduna su ci gaba da ragargazar romon dimokradiyya wanda suke kwankwada tun daga 2015 har zuwa yanzu.
Wasu ababe da ke ci wa wasu tuwa a kwarya a jihar sun hada da yadda gwamnatin ke fatattakar ma’aikata a duk lokacin da gwamnati ta ga damar yin haka. wannan matsala na damun mutane matuka sannan kuma gwamnati bata maida musu da wasu ayyukan ko kuma ta biya su hakkokin su. mutum zai wayi gari ne kawai ya ji wai sunar sa ta fito cikin sunayen wanda gwamnatin jihar ta sallama. Daga nan sai ya afka cikin rudanin gaske ya rasa inda zai saka kansa. Wannan matsala na dga cikin matsalolin da mutanen jihar Kaduna ke tsoro da shakka kada sai sun maido da APC su gwamnace kida da karatu.
Yanzu dai haka ya rage wa mai shiga rijiya, ko jama’a su canja wa kansu zani ko kuma su cigaba da daura tsohuwar atamfar da suka saba da ita aka kuma san su da ita.
Wasu da dama na ganin haka dai za su ci gaba da hakuri har kawai tunda sun saba da salon El-Rufai, iri sa suke so kuma shi za suyi a 2023.
Discussion about this post