Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dokokin Jihar Ondo, Oluwale Ogunmolasiyi, ya bayyana cewa aƙalla mahara sun kashe tsakanin mutum 70 zuwa 100, a wani mummunan harin da su ka kai a Cocin St. Fransis Katolika da ke Owo, Jihar Ondo.
Ogunmolasiyi wanda ya ce ya je cocin da kuma asibiti ya ga irin mummunan ɓarnar da maharan su ka yi, ya ce abin ya yi muni sosai.
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da harin. Shi ma Gwamna Rotimi Akeredolu na Ondo, ya ce harin shaiɗanci ne tantangarya.
Ƙungiyar Kiristoci ta Ƙasa CAN ta yi tir da harin, kuma ta tsine wa maharan.
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Ondo ya ce ya zanta da uwan wani yaro da ke da sauran kwana a gaba, wanda ya shaida masa cewa maharan Fulani ne makiyaya.
‘yan bindigar dai sun kashe maza, mata da ƙananan yara da dama, lokacin da su ka buɗe wuta a cikin cocin.
Wanda lamarin ya ritsa da shi ya ce sai da maharan su ka fara jefa gurneti a cikin cocin su ka firgita mutane, sannan su ka buɗe masu wuta.
Yayin da Ogunmolasiyi ya ce ya ga aƙalla gawarwaki 20 a idon sa, Babban Likitan Asibitin Tarayya da ke Owo, ya ce an kai gawarwakin mutane 23 a asibitin, sannan kuma akwai mutane da aka ji wa rauni da dama.