Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC ta liƙa sunayen ‘yan takarar shugaban ƙasa su 16 tare da bayanan inda kowanen su ya yi karatu ko aiki ko wani riƙe muƙami.
Sai dai abin mamaki, INEC ba ta bayyana komai ba a wuraren da ya kamata a bayyana makarantun da ɗan takara ya halarta, a ƙarƙashin sunan Bola Tinubu.
Ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar APC Bola Tinubu, ya ƙi aika wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC takardun shaidar ya kammala firamare, sakandare da jami’a.
Dama kuma haka ya taɓa yi wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa a 1999, lokacin da ya yi takarar gwamnan jihar Legas a ƙarƙashin jam’iyyar AD.
A wannan karo, Bola Tinubu bai ce komai ba. Amma dai ya rubuta wa INEC wasiƙar da ya haɗa da fam ɗin sa na takara, ya miƙa wa INEC. Wasikar na ɗauke da bayanin cewa:
“An sace min takardun makaranta na tun daga ma firamare har na sakandare da na jami’a, lokacin da na tsinci kai na cikin halin gudun hijirar tilas da na yi bayan Janar Sani Abacha ya hamɓarar da gwamnatin riƙon-ƙwarya a ranar 17 Ga Nuwamba, 1993.
“Kafin a hamɓarar da gwamnatin riƙon-ƙwarya a lokacin kuwa, ni ina Majalisar Dattawa ne, kuma ni ne Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗaɗe.
“Yayin da a lokacin bayan hawan Abacha mun matsa masa lambar neman ganin an dawo da dimokraɗiyya, ina cikin waɗanda aka kafa wa ƙahon-zuƙa, ana so a damƙe.
“Na gudu da yi gudun hijira a waje. Bayan na dawo cikin 1998, na taras an sace wasu muhimman kayayyaki na, ciki har da takardun shaidar kammala firamare, shaidar kammala sakandare da kuma kammala jami’a.”
A cikin takardar Tinubu ya rubuta cewa ya yi karatu a firamaren St. Paul Children’s Home School ta Ibadan a 1958 zuwa 1968.
Ya ce ya yi sakandare ta Government Collage Ibadan, 1965 zuwa 1965. Sannan kuma ya yi karatu a Kwalejin Richard Daley da ke birnin Chicago na Amurka. Kuma ya je Jami’ar Chicago.
Idan ba a manta ba, run cikin 1999 Tinubu ke fama da zargin kantara ƙarairayi a tsakardun makarantar sa.
An yi ta maka shi ƙara kotu a shekarun da ya ke Gwamnan Jihar Legas. A ƙarshe Ƙotun Ƙoli ta ce ba za a iya gurfanar da shi ba, saboda ya na da rigar kariya daga tuhuma.
Sabuwar Ƙara: Bayan Tinubu ya fito takara cikin watan Mayu ne kuma wata ƙungiya ta maka shi ƙara kotu, inda ta nemi a haramta masa shiga takara, saboda a cewar waɗanda su ka maka shi kotu, Tinubu ya yi ƙaryar kammala Jami’ar Jihar Chicago.
Har yanzu dai bayan ya lashe zaɓen fidda gwani, kotu ba ta ranar fara shari’ar ba.
Discussion about this post