A ranar Alhamis ne wani magidanci Kuma direban motar haya Irinsanmi Ayeniberu ya kai karar matar sa Chinwe a kotun Igando dake jihar Legas domin kotu ta raba auren sa na shekara hudu saboda rashin jituwa.
Ayeniberu wanda ke zama a lanba 15, hanyar African Mission dake Igando ya ce Chinwe wacce ya aura bayan rasuwar matarsa na farko masifaffiyace sannan bata girmama na gaba da ita.
“Da na da matarsa da ‘ya’ya na biyu maza duk sun bar gidana saboda yawan fadan Chinwe.
Ita ko Chinwe ta ce Ayeniberu karya yake fadi a kotun.
Ta ce Ayeniberu ya yi mata karya kafin ya aure ta.
“Ya ce idan ya aure ni zai kula da ni da ‘ya’yan da na haifa da tsohon mijina amma bai yi haka ba.
“Ayeniberu bai fada mun cewa auren zuba ruwa a buta muka yi da shi ba sai bayan da na dauki ciki na haifi da namiji a shekaran 2018.
“Bayan wannan dan ya rasu sai na sake daukar wani cikin amma Ayeniberu ya bani kwayoyin zubar da ciki cewa maganin gudawa ne.
“Na yi zuban jini har na tsawon makoni biyu kafin cikin ya zube.
“Ayeniberu ya ce abin kunya ne da tsufansa yana haihuwa sannan shi ya aure ni ne domin ya samu mai yi masa wanki, abinci da wacce zai rika saduwa da ita kawai ba ta zo ta rika suburbuɗa masa ƴaƴa ba.
Chinwe ta ce mijinta na yawan kiranta gwanjo sannan ‘ya’yan sa kan lakada mata dukan.
Ta ce Ayeniberu ya kawo kara kotu ne saboda ta ki yin amfani da dabarun bada tazarar haihuwa.
Alkalin kotun Koledoye Adeniyi ya ɗage shari’ar zuwa ranar 28 ga Yuni.
Discussion about this post