Bayanai na ci gaba da fitowa fili dangane da dalilin da ya sa ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin PDP, Atiku Abubakar bai ɗauki Gwamna Nyesom Wike matsayin mataimakin takarar sa ba, sai ya ɗauki Gwamna Ifeanyi Okowa na Delta.
Wike dai shi ne ya zo na biyu a zaɓen, wanda Atiku ya zo na ɗaya. Ya na daga cikin gwamnoni uku da jiga-jigan PDP su ka bai wa Atiku sunayen su domin ya ɗauki ɗaya daga cikin su. Sauran su ne Ifeanyi Okowa Gwamnan Delta da kuma Udom Emmanuel na Akwa Ibom.
Dukkan waɗannan ukun daga 2023 sun kammala zango na biyu na mulkin su a matsayin gwamnoni.
Atiku ya shaida wa manyan PDP cewa ba zai iya ɗaukar Wike ba, saboda baya ga cewa shi ne abokin kafsawar sa a zaɓen fidda gwani na 2023 ɗin.
Sannan kuma ya shaida masu cewa Wike ya yi ƙoƙari ya kayar da Atiku a takarar zaɓen fidda gwani a 2018, inda shi Wike ya goyi bayan Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto a wancan lokacin.
Sai dai kuma siyasa ta raba Tambuwal da Wike a zaɓen fidda gwani na 2022, inda Tambuwal ya janye wa Atiku kuma ya umarci mabiyan sa su zaɓi Atiku.
Wannan tuggu da Tambuwal ya shirya shi ne ya kayar da Wike, wanda bayan kammala zaɓe ya kira Tambuwal da ire-iren su maciya amana.
Majiya ta ce duk da Atiku ya kai ziyarar neman goyon baya a gidan Wike, a Abuja bayan kammala zaɓe, har Wike ya yi alƙawarin taimaka wa Atiku a zaɓen shugaban ƙasa, majiya ta ce hankalin Atiku ya tashi, ganin yadda bayan Wike ya koma Fatakwal ya riƙa antaya maganganu masu zafi kan gwamnonin da su ka zaɓi Atiku, musamman Tambuwal da Ifeanyi Okowa.
Wike ya ji haushin yadda Tambuwal ya kware masa baya, domin shi Wike a 2018 ya goya wa Tambuwal ɗin baya.
Sannan kuma Wike ya ji takaicin abin da Okowa ya yi, wato goyon bayan Atiku.
Dalilin haushin kuwa shi ne, Gwamna Okowa ne jagaba wajen gwagwarmayar da gwamnonin kudu su ka riƙa yi a baya cewa tilas sai ɗan kudu za a bai wa takara.
Tunda kuwa Wike ya fito takara, ya na ganin bai ga dalilin da zai sa Okowa ya umarci dukkan daliget na Delta su zaɓi Atiku.
Sannan kuma Atiku na zargin cewa Wike ya yi rigima da tsohon shugaban PDP na ƙasa, Uche Secondus ne, saboda Secondus ɗin ya kusanci Atiku sosai da sosai.
Wasu manyan PDP na ganin idan aka bai wa Wike takarar mataimakin shugaban ƙasa, hakan zai kakketa PDP, maimakon ƙara ɗinke ɓarakar jam’iyyar.
PREMIUM TIMES Hausa ta yi nazaein Abin da ɗaukar Ifeanyi Okowa zai janyo wa takarar Atiku a zaɓen 2023.
A ranar Alhamis da rana ce ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya gabatar da Gwamnan Delta Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakin takarar shugaban ƙasa ɗin sa a zaɓen 2023 mai zuwa.
Ɗaukar Ifeanyi Okowa matsayin mataimakin takarar shugaban ƙasa na PDP zai haifar da abubuwa da dama, waɗanda ko dai su kai Atiku ga nasara, ko kuma ya ƙara shan kaye, kamar yadda ya sha a baya har sau uku a zaɓen shugaban ƙasa.
Ko ma dai me kenan, lamarin zai yi tasiri ne ko rashin yin tasiri, bisa la’akari da irin yadda yi amfani da abubuwan.
Da farko dai masu ruwa da tsaki na yi wa Okowa kallon cewa natsatstsen mutum ne kuma kamili, ba kamar Gwamna Nyesom Wike da ake wa kallon ɗan gidoga ko ɗan hauragiya da harigido ba.
Can a jihar Delta dai lamarin siyasar za ta iya canjawa idan PDP ta samu nasarar kama mulki. Domin tun daga 1999 har yau tsohon Gwamna James Ibori ne ke yin uwa-makarɓiya wajen naɗa wanda zai yi gwamna a jihar.
Shi kan sa Okowa yaron gidan siyasar James Ibori ne, saboda a 1999 zuwa 2007 ya yi kwamishina ƙarƙashin gwamnatin James Ibori. Kuma ya yi Sakataren Gwamnatin Jihar Delta a zamanin gwamnatin Emmanual Uduiaghan.
Cikin 2011 Okowa ya ci zaɓen Sanata na Delta ta Arewa.
Sai dai kuma an samu saɓani a wannan zaɓen fidda-gwani na wanda zai gaji Okowa a gwamnan Delta ƙarƙashin PDP. Wanda Ibori ke so daban, shi ma Gwamna Okowa wanda ya ke so daban. Dukkan su kuma ƙabilar Urhobo ne, tushen James Ibori.
A ƙarshe dai ɗan takarar da Okowa ke so ya kayar da ɗan takarar da Ibori ke su. An ce Ibori ya fusata, har ya yi alƙawarin idan zaɓe ya zo sai ya shuka wa PDP ko kuma ɗan takarar tana jihar tsiya.
To yanzu dai tunda an zaɓi Okowa ɗan takarar mataimaki, jam’iyyar PDP ta koma a hannun sa kenan a jihar Delta, maimakon ubangidan sa James Ibori.
Abu na biyu shi ne ana ganin matsayin Okowa ɗan asalin ƙabilar Igbo, hakan zai iya yayyafa wa yankin Kudu maso Gabas ruwan sanyi, su haƙura su goyi bayan PDP, tunda dai ba su samu damar tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa ba a manyan jam’iyyu biyu, APC da PDP.
Amma shi kuwa Wike, ba sau ɗaya ko sau biyu ba ya sha nesanta kan sa ko asalin sa daga kabilar Igbo.
Sannan an ce Wike ne ya riƙa sukar Peter Obi har ya harzuƙa shi, ya fice daga PDP, ya koma LP ya fito takarar shugaban ƙasa.
Okowa bai cika surutai ko bobbotai irin na Wike ba. Ana ganin Wike ya yi katoɓara a shekarun baya da ya ce “Jihar Ribas ta Kiristoci ce zalla.”
Shi kuwa Gwamna Okowa babu ruwan sa da shiga-sharo-ba-shanu, ko yin uwa-makarɓiyar rigingimun siyasa, kamar yadda Gwamna Wike ke yi, har abin ya zame masa jiki.
Babban aikin da ke gaban Okowa shi ne yadda zai samar wa PDP ƙuri’u a Kudu maso Gabas, Kudu maso Yamma da Kudu maso Kudu. Zai iya yin bakin ƙoƙarin sa, musamman tunda bai taɓa shiga hancin manya da ƙudundune ba.
An haifi Okowa a cikin 1959 a garin Owa-Alero, cikin Ƙaramar Hukumar Ika ta Arewa maso Gabas.
Sai dai kuma masu nazarin siyasa da dama na ganin a yanzu PDP za ta iya rasa ɗimbin ƙuri’un magoya bayan Gwamna Wike, ganin yadda ya samu ƙuri’u da dama a zaɓen fidda gwani.
Su na ganin da shi aka ɗauka, zai fi karɓuwa har a Arewa sosai. Domin a cewar da dama, ba a san Ifeanyi Okowa a Arewa ba.
Ya yi kwamishina zamanin mulkin James Ibori, ya yi Sakataren Gwamnatin Jiha zamanin mulkin Emmanual Uduiaghan, kuma ya yi sanata kafin ya zama gwamna.
Discussion about this post