Fadar Shugaban Ƙasa ta maida wa Bola Tinubu raddi, kwanaki huɗu bayan ya yi wa Shugaba Muhammadu Buhari gorin cewa ya yi takara sau uku ya na faɗuwa, sai da Tinubu ya mara masa baya sannan ya yi nasara a 2015 da 2019.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran Shugaba Buhari, Garba Shehu ya fitar, ya ce miliyoyin ‘yan Najeriya ne su ka zaɓi Buhari, ba wai mutum ɗaya ba.
Shehu ya ce mutane da dama sun taimaka wajen yin rawar ganin Buhari ya zama shugaban ƙasa, kuma akwai manya da ƙanana sosai.
Ya ce wannan gagarimar nasara ta kafa tarihin da a karon farko ɗan adawa ya kayar da shugaban da ke kan mulki a ƙasar nan.
A ranar Asabar dai Tinubu ya fitar da sanarwar cewa ya na ganin girma da mutuncin Shugaba Muhammadu Buhari.
Ya ce ba a yi wa jawabin da ya yi da Yarabanci kyakkyawar fassara ba.
Garba Shehu ya bayyana jawabin da Tinubu ya yi cewa ba abin mamaki ba ne.
“Tun da farko akwai waɗanda su ka shawarci shugaban ƙasa cewa ya sake tsayawa takara, duk kuwa da ya faɗi sau uku.
“Waɗannan su ne waɗanda su ka ga akwai buƙatar a kafa wata jam’iyya, wato APC, wadda za ta iya kasancewa motar da za a hau a kai ga nasara a inda gamayyar jam’iyyun adawa ha su kai ga nasara ba kafin ita.”
Shehu ya ce wannan tunani ya samu karɓuwa a zukatan miliyoyin jama’a, har su ka zaɓi APC ta yi nasara.”
Raddin Shehu ya zo ne daidai a ranar jajibirin Gangamin APC, wanda za a zaɓi ɗan takarar shugaban ƙasa.
Tinubu na cikin ‘yan takara 23 da ke nema. Kuma Abuja ta cika ta batse da mahalarta gangamin, inda tun daga ranar Lahadi ake ta ƙulle-ƙullen neman yadda za a fitar da ɗan takara ba sai a kai ga yin zaɓe ba.
Gwamnonin Arewa na APC dai sun amince a bai wa Kudu takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar kawai a wuce wurin.
Sai dai kuma kalaman Shugaban APC Abdullahi Adamu da ya ce sun yarda a bar wa Sanata Lawan daga Arewa takara, ya tayar da ƙura, har shugabannin APC sun ce ba su amince da maganar ta sa ba, domin ba a tattauna haka a wurin taro ba.