Sannu a hankali dai Majalisar Dattawa ƙoƙari ta ke yi ta koma wani dandalin da tsoffin gwamnoni ke mamayewa su na zaman-dirshan bayan kallama wa’adin shekarun su takwas kan muƙamin gwamna.
A wannan Majalisar Dattawa da ke kai a yanzu, akwai tsoffin gwamnoni 14 a cikin ta.
Amma kuma a yanzu akwai tsoffin gwamnoni da kuma waɗansu da ke shirin kammala wa’adin mulkin su, su tafi Majalisar Dattawa su yi ritaya a can, har su 28, maimakon su tafi su yi zaman su a gida.
Waɗannan gwamnoni 28, wasu tsoffi ne, wasu na kan mulki, wasu kuma su na cikin majalisar, amma kuma sun ƙi gajiya da zaman majalisa, za su sake tsayawa takara a zaɓen 2023.
Da ya ke Majalisar Dattawa ba ta da wa’adin daina yin sanata, ba kamar Gwamna ba mai cikakken ‘yancin shekaru takwas na zango biyu kenan.
Wasu sanatocin sun daɗe a Majalisar Dattawa ana damawa da su. Kamar Kabiru Gaya da Adamu Aliero, Ɗanjuma Goje da sauran su.
A wannan Majalisar Dattawa da ke kan mulki dai tsoffin gwamnoni 14. Amma idan aka dubi yawan sanatoci 28 masu neman takara, idan su duka su ka ci zaɓen 2023, to Majalisar Tarayya mai Sanatoci 109, kashi 1 bisa 4 na Dattawan Majalisa duk za su kasance tsoffin gwamnoni kenan.
Tsoffi Da Gwamnonin Da Ke Ci 28 Masu Takarar Sanata A Zaɓen 2023:
Adams Oshiomhole
David Umahi
Aminu Tambuwal
Darius Ishaku
Samuel Ortom
Okezie Ikpeazu
Abubakar Sani Bello
Ibrahim Ɗanƙwambo
Abdul’aziz Yari
Ifeanyi Ugwuanyi
Simon Lalong
Gbenga Daniel
Aliyu Wammako
Kabiru Gaya
Chimaroke Nnamani
Tanko Almakura
Ɗanjuma Goje
Kashim Shettima
Ibrahim Geidam
Siriake Dickson
Saminu Tiraki,
Gabriel Suswan
Ibrahim Shekarau
Adamu Aliero
Sam Egwu
Atiku Bagudu
Godswill Akpabio.
Discussion about this post