Majalisar Magance Matsalar Abinci ta Ƙasa za ta yi taro domin shawo kan tsayar kayan abinci a cikin ƙasar nan.
An dai kafa wannan majalisa ce a cikin 2018, kuma Shugaba Muhammadu Buhari ne shugaban ta.
Sauran mambobin sun haɗa da wasu gwamnoni, Ministan Gona da Raya Yankunan Karkara, Ministan Zuba Jari da Kasuwanci da wasu da dama.
Akwai kuma MInistan Harkokin Kuɗaɗe da na Kasafin Kuɗi da Tsare-tsare.
An kafa kwamitin ne domin ya gaggauta kawar da matsalolin Fulani da makiyaya.
Sai kuma canjin yanayi da irin yadda ya ke shafar yankunan da ake noma.
Sai kuma magance matsalar wuraren kiwo, tafkuna, kogi, gurɓata yanayi da kamfanonin haƙar mai ke haifawa a Neja Delta, kula da matsalar ‘yan bindiga, sumogal da sauran su.
Rabon da kwamitin ya yi taro tun cikin Satumba, 2020.
Ministar Harkokin Kuɗaɗe Zainab Ahmed ce ya sanar cewa za a yi taron ne domin bijiro da hanyoyin rage tsadar farashin kayan abinci.
Tun cikin 2021 ne kayan abinci su ka yi tsadar da har yau bai sake yin ƙasa ba.
Discussion about this post