Rundunar Sojojin Najeriya ta yi rashin wani jami’in ta mai muƙamin Manjo, a wani harin da ‘yan ta’adda su ka kai masu a cikin Ƙaramar Hukumar Mariga ta Jihar Neja.
‘Yan ta’addar sun yi wa sojojin kwanton-ɓauna ne a lokacin da su ke cikin jerin gwanon jami’an tsaro daidai wani ƙauye da ake kira Rijiyan Daji.
Majiyar da ba ta so a ambaci sunan ta, ta ce a ranar Laraba ce lamarin ya faru, inda ɓangarorin biyu su ka buɗe wa juna wuta.
Sojojin dai daga Makarantar Horo da Bada Atisaye da Cusa Aƙidar Kishi (TRADOC) su ke.
Majiya ta tabbatar da cewa an rasa ran wani soja mai muƙamin Manjo, wani sojan ba a san inda ya ke ba.
An kuma ji wa uku rauni sanadiyyar harbin bindiga da ‘yan ta’addar su ka yi masu.
Wata majiyar kuma ta ce Manjo ɗin da aka kashe an garzaya da shi asibitin Kontagora, amma rai ya yi halin da kafin a kai ga ceton ran na sa.
Baya ga kisa da raunata wasu sojoji, ‘yan ta’addar sun arce da motar sojin guda ɗaya, samfurin Toyota Hilux, kuma sun gudu da manyan makamai.
Jihar Neja na sahun jihohin Kaduna, Katsina, Zamfara, Sokoto da Kebbi, jihohin da ‘yan bindiga su ka hana zaman lafiya fiye da shekaru bakwai zuwa yau.