Tsohon gwamna jihar jihar Kano, kuma ɗan takarar shugaban Kasa na jam’iyyar NNPP Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa jam’iyyar NNPP da LP na tattaunawar yiwuwar haɗewa domin tunkarar zaɓen 2023.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a hira da yayi da BBC Hausa ranar Asabar.
” Lallai muna tattaunawa, ganin cewa da PDP da APC babu wanda ya zaɓi mataimakin ɗan takara daga Yankin Kudu Maso Gabas. A dalilin haka muke ganin idan muka haɗe abin zai yi tasiri.
” Cikin mu ɗaya ne zai yi takara ɗaya kuma ya yi mataimaki.
Sai dai kuma Kwankwaso bai faɗi ko waye zai zama liman ba, da kuma na’ibi. ” Babba dai babba ne, idan har haɗewar ya tabbata kowa ya san babba shine zai shiga gaba ƙarami kuma ya na biye da shi. ”
Zuwa yanzu Kwankwaso ya ce jam’iyyun sun mika sunayen wasu na wucin gaɗi wanda za su tsaya musu kafin su gama amincewa a tsakanin su su fito takarar na mai gaba ɗaya.
” Muna da kwanaki kusan 40 da za mu cigaba da tattaunawa a tsakanin mu domin fidda ainihin sunayen waɗanda za su zama mataimakin shugaban kasa. Daga yanzu zuwa lokacin za mu kammala tsaretaren mu mu samu matsaya guda ɗaya.
Masu yin sharhi na ganin wannan hadewa zai iya yin tasiri matuka ganin dukkan su ƴan siyasan na da mabiya masu ɗinbin yawa a faɗin kasar nan.
Discussion about this post