Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta ɗaure abokan daƙa-daƙar safarar ƙwayoyin Abba Kyari, ɗaurin shekaru biyu kowanen su.
An tuhume su inda aka same su da laifi a tuhuma ya 5, 6 da ta 7. Mai Shari’a Emeka Nwete ya ɗaure su biyu ɗin kowane shekaru biyu a tuhuma ta 5, shekaru biyu a tuhuma ta 6, kuma shekaru biyu a tuhuma ta 7.
Sai dai kuma kotu ta ce za su yi shekaru 6 ɗin kowanen su a a cikin shekaru 2 kacal. Wato kwanakin ɗaurin kowane hukunci za su tafi da sauran kwanakin kenan.
Sannan kuma kotu ta ce za su fara zaman kurkui za a lissafa tun daga ranar da jami’an tsaro su ka kama su cikin watan Maris a Filin Jirgin Sama na Akanu Ibiam da ke Enugu.
Yadda Dillalan Kwayar Su Ka Amsa Laifin Su A Kotu:
Dillalan hodar sun amsa laifin su, Kyari da sauran ‘yan sanda ba su amsa laifi ba.
Waɗanda ke cikin zauren shari’ar da aka fara ta su Abba Kyari a Babbar Kotun Tarayya, Abuja, sun cika da mamaki, yayin da mutum biyu da ake zargin sun shigo da hodar ibilis daga Brazil da Habasha, su ka amsa laifin su, ba tare da wata jayayya ba.
Chibunma Patrick da Emeka Alphonsus Ezenwanne sun amsa laifin tuhuma mai lamba ta 5, 6 da na 7, waɗanda duk ke da nasaba da laifin shigo da muggan ƙwayoyi.
“Ran Mai Shari’a Ya Daɗe, na aikata laifin.” Haka kowanen su ya sanar wa kotu a ba’asin su da aka shigar daban-daban.
An karanta masu cewa sun karya dokar Hukumar NDLEA, ta Sashe na 14(b), ta 30 a ƙarƙashin Dokar 2004.
An tuhume-tuhume su da shigo da koken a filin jiragen sama na Akanu Ibiam da ke Enugu, a ranar 25 Ga Janairu, 2022.
PREMIUM TIMES ta bada labarin NDLEA sun gurfanar da Abba Kyari a kotun Abuja.
Jami’an Hukumar NDLEA sun gurfanar da dakataccen Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda, Abba Kyari a Babbar Kotun Tarayya ta Kaduna.
An shiga da shi kotun sa safiyar Litinin misalin ƙarfe 8:12 na safiya.
An gabatar da shi ne bisa zargin sa tare da wasu jami’an ‘yan sanda huɗu da laifin safara da kuma tu’ammali da hodar ibilis mai nauyin kilogiram 22.35.
NDLEA sun kama shi tare da ‘yan sandan huɗu waɗanda su ma ke ƙarƙashin sa a lokacin da ya ke shugaban ‘Yan Sandan Kai Ɗaukin Gaggawa masu kamen ‘yan damfara da garkuwa da mutane.
Kafin NDLEA ta kama shi, Kyari ya shafe watanni shida a dakace, bayan zargin sa da haɗa baki da gawurtaccen ɗan damfara Hushpuppi.
An zarge shi da shirya damfarar dala miliyan 1.1, lamarin da ya janyo Amurka ke neman a tura a can ta yi masa hukunci a Amurka.
A zaman shari’a, su Kyari za su fuskanci tuhumar amfani da kuma mallakar hodar Ibilis ba bisa ƙa’ida ba.
Sannan akwai wata hutuma da ake wa Kyari shi kaɗai, wadda ake zargin sa da bai wa babban jami’in NDLEA toshiyar bakin Dalar Amurka 61,400 don kada NDLEA ta bincika kuma kada ta auna wata hodar Ibilis don kada a gane ko mece ce.
Manyan ‘yan sanda huɗu da ake tuhuma tare da Kyari sun haɗa da Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda Sunday Ubua, Mataimakin Sufurtanda Bawa James, Sufeto Simon Agirgba, Sufeto John Nuhu.
Akwai fararen hula biyu, Chibunma Patrick da Emeka Alphonsus Ezenwane. Su ne ake zargin sun shigo da hodar Ibilis mai nauyin kilogiram 21.35.