Kotu a jihar Jigawa ta yanke wa wani mutum mayaudari wanda aka samu yana gauraya taki da kasa ya ɗinke buhunan sannan ya saida wa manoma a Jigawa hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni shida.
Alkalin kotun Mannir Abdullahi ya yanke wannan hukunci ne bayan Turaki mai shekaru 40 ya amsa laifinsa.
Alkali Abdullahi ya ce Turaki zai yi zaman kurkuku na tsawon watanni shida ko Kuma ya biya kudin belin Naira 80,000.
Sannan ko zai biya wannan beli Alkali ya ce sai Turaki ya yi zaman gidan yari na tsawon makonni uku domin ya zama darasi a hareshi da wasu masu aikata irin haka.
“Turaki zai iya biyan kudin belin idan har ya nuna cewa ya zama mutum na gari ko Kuma ya yi zaman gidan yari na tsawon watanni uku.
Kotu ta Kuma kwace buhunan takin.
A jawabin sa kakakin rundunar NSCDC dake jihar Jigawa Adamu Shehu ya ce jami’an hukumar sun kama Turaki ranar 4 ga Yuni a karamar hukumar Hadeja da buhun takin NPK guda daya da ya hada da ƙasa zai siyar.
Shehu ya ce bincken da suka gudanar ya nuna cewa Turaki na da buhunan taki 7 dake ajiye a gidansa wanda zai na riƙa amfani da su yana damfarar mutane.
“Rundunar ta gano cewa bayan ya hada da takin da ƙasa yakan siyar wa manoma takin akan farashin da ake siyarwa a kasuwa wato naira 16,000.