Kotun majistare dake Abeokuta ta yanke wa Sakiru Famuyiwa mai shekara 38 hukuncin zama a gidan kaso na tsawon shekaru 7 bayan an kama shi da laifin yin garkuwa da ‘yar shekara uku a coci.
Kotun ta gurfanar da Famuyiwa bisa laifuffukan Sata da tada hankalin jama’a.
Alkalin kotun S. S Shotayo ya ce ya yanke wannan hukunci ne bisa ga hujojjin da fannin da suka shigar da kara suka gabatar wanda ya tabbatar wa kotun cewa Famuyiwa ya aikata laifin da ake zarginsa da shi.
Shotayo ya ce a dalilin haka kotu ta yanke wa Famuyiwa hukunci zaman kurkuku na shekara bakwai tare da yin aiki mai wahala.
Dan sandan da ya shigar da karan Olaide Rawlings ya ce Famuyiwa ya aikata haka ne ranar 15 ga Afrilu yayinda ake sujadan kyakyawar Juma’a a ‘Celestial Church of Christ’ dake hanyar Igbore Ijeja a Abeokuta.
Sujadan kyakyawan Juma’a sujada ne da kiristoci a fadin duniya ke yi gab da Easter.
“Kowa a Cocin na sanye da farafen kaya amma shi Famuyiwa ya shigo cocin da kayan gida sannan ya wuce zuwa bangaren Yara ya kama hannun daya zai waske da ita.
“Garin haka ne wani cikin malaman yaran ya gano shi inda kafin Famuyiwa ya fice daga cocin mutane suka kama shi.
“Da ya shiga hannu sai Famuyiwa ya ce dama ya zo cocin neman wani Fasto John wanda shine mahaifin yarinyar da zai waske da ita.
“An tara duk fastocin cocin domin ya nuna wane fasto John da ya ce ya zo nema amma bai iya haka ba.
“Daga nan aka damka shi hannun ‘yan sanda domin a ci gaba da bincike.