Kotun gargajiya dake ‘Grade A’ a Iyaganku ta
yanke wa wani Kansila hukuncin dauri ma tsawon watanni Uku.
Kansilan mai shekaru 53 Muyiwa Ojo-Osagie ya lakada wa mahaifiyar matar sa Mrs Sarah Gbadebo dukan tsiya Sannan ya yi barazanar sai ya kashe ta.
Alkalin kotun Mrs Basirat Gbadamosi ta yanke wa Ojo-Osagie hukuncin ɗauri na tsawon watanni uku a kurkuku bisa laifin yi wa sirikansa duka ko ya biya tarar Naira 20,000.
Laifin yi wa sirikansa barazanar kisa Ojo-Osagie zai yi wa al’amuma aikin watanni biyu sannan ya rubuta wasika ga sirikansa Mrs Gbadebo domin neman afuwarta.
Dan sandan da ya shigar da kara a kotu Kola Olaiya ya ce Ojo-Osagie ya daki sirikan sa Mrs Gbadebo mai shekara 81 da lema a ranar 11 ga Agusta 2019 da misalin karfe 10:30 na safe.
Olaiya ya ce Ojo-Osagie ya aikata haka ne bayan ya gano cewa tsohuwar matarsa ta kwashe ‘ya’yan sa biyu mata bayan auren su ya mutu.
Ya ce yi wa sirikansa barazanar kisa da Ojo-Osagie ya yi na neman tada zaune tsaye.
Olaiya ya ce cin mutuncin da Ojo-Osagie ya yi ya saba dokar hukunta masu aikata laifuka irin haka na sashe 249 (d) da 351 na jihar Oyo.
Discussion about this post