Kotu dake kauyen Iyaganku a Ibadan jihar Oyo ta yanke wa Isaac Dumabara mai shekara 23 hukuncin zaman gidan yari na tsawon wata daya bayan ta kama shi da laifin sace tukunyar miyan dage-dage.
Tukunyan miyan dage-dagen da Dumabara ya sace na dauke da naman naira 40,000 a ciki.
Alkalin kotun S.A Adesina ya yanke wannan hukunci ne ba tare da ya bashi zabin biyan kudin beli ba.
Dan sandan da ya shigar da karar Sikiru Ibrahim ya bayyana a kotu cewa Dumabara ya sace tukunyar miyan a shagon siyar da abinci na ‘Pleasure Summit’ dake hanyar Magara a Iyaganku Ibadan.
Ibrahim ya ce wannan ba shine karon farko ba da Dumabara ke sace-sace a shagon ba.
Ya ce Dumabara ya saci tukunyar iskar gas guda uku, stabiliser daya da takalmi kiran ‘Adidas’.
Ibrahim ya kuma ce Dumabara ya saci talabijin mai girman inci 42 da kudinsa ya kai Naira 200,000 duk a wannan shagon siyar da abincin.
Ya ce laifin da Dumabara ya aikata ya sabawa doka na jihar Oyo na shekarar 2000.
Discussion about this post