Babban Kotu dake Birnin Kudu a jihar Jigawa ta yanke wa Ibrahim Abdullahi hukuncin daurin rai da rai bayan ta kama shi da laifin yi wa dan shekara shida fyade.
Kakakin ma’aikatar shari’a Zainab Baba-Santali ta bayyana haka a sanarwa ranar Juma’a.
Zainab ta ce Abdullahi mai shekara 27 kuma mazaunin kauyen Garu ne dake garin Dutse sannan ya aikata wannan ta’asa tun a watan Fabrairun 2021.
Ta ce Abdullahi kan lallabi yaron zuwa dakinsa ko Kuma a ofishinsa dake makaranta inda yake lalata da shi ta dubura.
“Dubun Abdullahi ya cika a ranar da wani malamin makaranta ya ga yaron ya fito daga ofishin Abdullahi yana tafiya wani iri sannan cikin lokaci kadan sai ga Abdullahi ya fito yana gyara wandonsa.
“Sakamakon binciken da makarantar ta gudanar ya nuna cewa Abdullahi na lalata da yaron ta baya.
“Bangaren da suka shigar da kara sun gabatar da shaidu hudu da sakamakon gwajin da aka yi wa yaron sannan Abdullahi ya gabatar da shaidu biyu da suka kare sa a kotun.
Alkalin kotun Musa Ubale ya yanke wa Abdullahi hukuncin daurin rai da rai.
Bayan haka Zainab ta ce a ranar 31 ga Mayu babban Kotu a Hadeja ta kuma yanke wa Aliyu Suleiman hukuncin daurin rai da rai bayan ya yi wa ‘yar shekara 12 fyade a karamar hukumar Birniwa.
Discussion about this post