Idan ba a manta ba gwamnatin jihar Kaduna ta kori malaman firamare sama 2000 a cikin makon jiya saboda wai basu zauna rubuta jarabawar kwarewa da gwamnati ta shirya ba.
Cikin waɗanda aka kora har da shugaban kungiyar na kasa Amba Audu wanda shima bai zauna rubuta jarabawar ba.
Shugaban ƙungiyar ya umarci malamai da su kaurace wa jarabawar saboda babu dalilin sake rubuta irin wannan jarabawa bayan an taɓa rubuta irinshi a shekarun baya.
Dalilin haka Audu ya ki rubuta jarabawar da wasu malamai sama da 2000.
Sai dai kuma gwamnatin Kaduna a cikin makon jiya ta sanar da korar duk wanda bai rubuta jarabawar ba da ya haɗa da shugaban kungiyar na kasa.
Kungiyar malamai NUT ta ce ta na tare da shugaban ta kuma ba za ta yi kasa-kasa ba wajen tabbatar da cewa gwamnati ta dawo da malaman da ta kora.
Mataimakin shugaban ƙungiyar na kasa Kelvin Nwankwo ya ce ” Ko El-Rufai ya maida malaman aikin su ko kuma kungiyar malaman ta shiga yajin aiki na kasa baki ɗaya. Ba za mu bari a ci mutunci malamai haka kawai ba da sunan wai basu rubuta jarabawar gwaji.
” Za mu kare hakkin malamai da kuma shugaban mu da gwamnatin jihar ta ci wa mutunci.
” Saboda cin mutunci da tonon silili, tun kafin a aika wa shugaban mu takardar sallama, har an sassaka takardar sallamar sa aiki a shafukan yanar gizo inda anan ma ya fara gani. Toh gwamnati ta sani muna tare da shugaban mu, babu gudu ba ja da baya.
Nwakwo ya kara da cewa abin ɓacin rai a ciki ma shine ” Maganar na Kotu, kotu ta umarci El-Rufai ya dakatar da korar ma’aikata sannan janye shawarar gudanar da sabuwar jarabawa sai an gama zama a kan maganar, amma yayi kememe, ya yi buris, ya fatattaki malaman da ke fama da tsananin matsalolin rayuwa da ake ciki.
Discussion about this post