Ɗan takarar shugaban ƙasa a jami’yyar NNPP Kuma tsohon gwamnan jihar Kano Rabi’u Kwankwaso ya ziyarci sarkin Owo Ajibade Ogunoye domin yi masa ta’aziyyar kisan gillar da aka yi wa mutane a coci ranar 5 ga Yuni.
Idan ba a manta ba a wannan rana ‘yan bindiga sun yi wa mabiya masu ibada a Cocin Katolika na St Francis dake Owo a jihar Ondo kisan gilla inda mutum 40 suka mutu sannan wasu da dama suka ji rauni.
Kwankwaso ya kuma ziyarci fadan sarkin Ijebu dake Owo inda ya yi wa basaraken da mutanen garin ta’aziyyar rasuwar mutanen.
Ya kuma ziyarci cocin St Francis da ‘yan bindiga suka kashe mutane da dama a wannan rana.
Kwankwaso ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta zage damtse wajen kare rayuka da dukiyoyin mutane a kasar nan.
Ya kuma jinjina wa gwamnan jihar Rotimi Akeredolu bisa matakan da ya ɗauka don n sammar da tabbatacciyar tsaro a jihar.
Baya ga Kwankwaso dan takaran shugaban ƙasa na jami’yyar APC Bola Tinubu ya ziyarci garin inda ya bai wa mutanen da harin ya ritsa da su gudunmawar naira miliyan 50 sannan ya bai wa cocin St Francis gudunmawar naira miliyan 25.
Shima mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo ya kai wa jihar irin wannan ziyara.
Discussion about this post